1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar shara mai guba a duniya baki daya

Mohammad Nasiru AwalSeptember 13, 2006

Duk da yarjejeniyar da ta tanadi zubar da shara mai guba a wuraren da suka dace amma wasu batagari ba sa aiki da ita.

https://p.dw.com/p/BtyC
Shara mai guba a Abidjan
Shara mai guba a AbidjanHoto: picture-alliance/dpa

“Mu dai a nan Kodivuwa ba mu da kudin da zamu taimakawa wadanda suka shaki iskar mai guba.”

Wannan dai wani dan Ivory Coats ke nan yake bayyana hushin jama´ar kasar baki daya dangane da shara mai guba da aka jibge a unguwanni da dama na birnin Abidjan.

Wannan batu na shara mai guba ba shi ne na farko ba. A shekara ta 1988 Italiya ta jibge wasu ganguna 2000 na shara mai guba a gabar tekun Nijeriya. Sannan a 1992 Jamus ta kai sharar maganin kashe kwari mai nauyin tan 350 a kasashen Romaniya da Albaniya, amma a tilas daga baya ta kwashe su bayan da wannan abin kunya ya fito fili. Wannan lamarin dai ba kawai wani bala´i ne da ya shafi muhalli da kuma dan Adam ba, a´a ya karya ka´idojin yarjejeniyar kasa da kasa ta birnin Basel, wadda aka cimma a shekarar 1989.

Yarjejeniyar wadda kasashe 160 suka sanyawa hannu, ta tanadi hanyoyin da suka dace na zubar da shara mai guba. Yarjejeniyar ta Basel ta kuma haramta tura shara mai guba zuwa kasashe masu tasowa inda babu wani tanadi na kawad da wannan shara a hanyoyin da suka dace. Hakazalika yarjejeniyar ta tilastawa kasashe ba da cikakken bayani na shara mai guba da zasu yi jigilarsa daga wani wuri zuwa wani wurin. Pierre Portas na biyu a ofishin dake kula da yarjejeniyar dake birnin Vienna ya ce wannan tsari na sa ido na aiki kwarai da gaske.

“Kowace kasa na da hukumar dake kula da shige da fice shara a cikin kasarta. Duk da cewa da akwai gyare gyare, to amma tsarin na aiki sosai.”

Don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu bisa manufa, wasu yankunan sun cimma yarjeniyoyi, wato kamar yarjejeniyar birnin Bamako wadda kasashen Afirka 12 suka rattabawa hannu da nufin kare muhalli da kuma al´umominsu daga shara mai guba. Ko da yake akwai irin wadannan yarjeniyoyi da yawa, amma ba sa wani tasiri wajen hana bata-gari yin jigilar sharar.

Kamfanonin sun bullo da sabbin dubaru na jibge shararsu a kasashe masu tasowa ba tare da hakan ya fito fili ba, inji Oumar Cisse na cibiyar ba da bayanai game da sinadari da wasu abubuwa masu hadari dake birnin Dakar.

Ya ce “A kasashe da babu su da kwarewa ta binciken abubuwan dake kunshe cikin kayakin da ake shigo musu da shi, ana ba su bayanai da suka saba da kayan da ake tura musu, inda a lokuta da dama akan sayar musu da shara a matsayin danyun kaya ko kayan gyara.”

Tsofaffin magungunan kamar na kashe kwari da aka haramta amfani da su a Turai, akan tura su kasashen gabashin Turai a matsayin wata gagarumar gudunmawa ta taimakon raya kasa. Yayin da ake tura tarkacen kayan lantarki a matsayin kayan da aka sake sabuntawa zuwa Afirka da Asiya.

A cikin watan nuwamba za´a fadada yarjejeniyar birnin Bamako, inda ake sa ran za´a dauki sahihan matakai na hana jibge shara mai guba da tarkacen masana´antun kasashe masu arziki a kasashe masu tasowa.