1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar samun bisa za ta hana matasan Afirka da dama halartar taron matasa na duniya a birnin Kolon.

YAHAYA AHMEDAugust 10, 2005

Yayin da birnin Kwalan ke kammala shirye-shiryen karbar bakwancin dubban matasa daga sassa daban-daban na duniya, wadanda za su halarci taron matasa na duniya da darikar Katolika ta shirya, rahotanni na iso mana cewa, darurukan matasa daga nahiyar Afirka ba su sami biza daga ofisoshin jakadancin Jamus da ke kasashensu don halartar taron ba. Wannan kuwa na da jibinta ne da shakkun da jami’an ofishin jakadancin ke nuna wa `yan Afirka gaba daya, na cewa, idan an ba su bizar suka zo nan Jamus, sai su buya ba za su dawo gida ba kuma. Amma wai shin, haka lamarin yake, ko dai, wani shinge ne na gama gari da ofisoshin jakadancin ke gindaya wa maneman biza daga nahiyar Afirka ?

https://p.dw.com/p/BvaY
Taron matasan katolika na duniya da aka yi a birnin Toronto na kasar Kyanada a shekara to 2002
Taron matasan katolika na duniya da aka yi a birnin Toronto na kasar Kyanada a shekara to 2002Hoto: AP

Kwanaki kadan kafin a fara taron matasa na duniya da darikar katolika ta shirya a birnin Kwalan, ana ta samun kararraki daga nahiyar Afirka da kuma Asiya, inda masu niyyar halartar wannan taron ke ta kara huskantar matsaloli wajen samun bizar shigowa nan Jamus. Kafofin cocin katolikan na nan Jamus da yawa ne ke ta kara nuna bacin ransu game da tsauraran matakan da ofisoshin jakadancin Jamus din ke dauka a kan maneman biza daga kasashe masu tasowa musamman ma dai na nahiyar Afirka da Asiya.

Babban ofishin manyan limaman kirista na darikar katolikan na lardin Limburg, ya zargi ofisoshin jakadancin Jamus din da gindaya wa dimbin yawan matasa daga nahiyar Afirka masu niyyar halartar taron na birnin Kwalan shinge, wajen ba su biza. Rahotanni kuma sun nuna cewa, a wasu kasashen Asiya ma haka lamarin yake. A lal misali, jaridar die Tageszeitung, wadda ta yi dogon sharhi a kan wannan batun, ta ce kusan `yan kasar Phillipine dari 6 ne ofishin jakadancin Jamus a birnin Manila ya hana su biza ba tare da ba su dalilin yin hakan ba.

Kazalika kafofin kula da huldodi da matasan katolikan na nan Jamus da na sauran kasashen duniya sun bayyana takaicinsu ga halayen da ofisoshin jakadancin Jamus din ke nunawa a kasashen Afirka. Wani kakakin ofishin bishop-bishop na darikar katolika na nan Jamus, Michael Wittekind, ya bayyana cewa, matasa da dama daga kasashen Senegal, da Kamaru da Togo ba za su iya halartar taron ba, saboda hana su biza da ofisoshin jakadancin Jamus a wadannan kasashen suka yi. Kakakin dai ya kara bayyana cewa, wannan abin mamaki ne, saboda tuni ofishin kula da tsara shirye-shiryen taron, ya cim ma yarjejeniya da ma’aikatar harkokin wajen Jamus, don saukaka wa masu niyyar halartar wannan taron dawainiyar neman bizar. Bisa wannan yarjejeniyar dai, matasan da za su halarci wannan taron kawai, ba za su biya kudin biza da a galibi ake karba ba. Kazalika kuma, ba sai ko wannensu ya sami takardar gayyata daga nan Jamus kafin ya cike takardun neman bizar ba. Ofishin tsara shirye-shiryen taron ya ba da takarda ta bai daya wadda ke bayyana shirinsa na daukar duk nauyin matasan da aka yi rajistarsu tun da farko, na cewa za su halarci taron, wajen ba su masauki, da abinci, da kuma kula da kiwon lafiyarsu, idan suka bukaci ganin likita a duk tsawon lokacin taron. Idan ta kama za a mai da su gida ma, saboda wasu dalilan, ofishin ya dau alakawarin biyan kudaden da za a kashe wajen daukar wannan matakin.

Amma duk da hakan, sai ga shi ofisoshin jakadancin na nuna wani halin da bai dace da yarjejeniyar da aka cim ma ba.

Bisa dukkan alamu dai, ofisoshin na taka tsantsan ne ta yin la’akari da abin da ya wakana a irin wannan taron da aka yi a birnin Toronto na kasar Kyanada a shekaru 4 da suka wuce. Rahotanni na nuna cewa, a wannan lokacin, mahalarta daga kasashe masu tasowa sun tsere daga taron, suka je neman mafaka. Gaba daya dai kusan mutane dari 8 ne suka mika takardunsu na neman mafaka a Kyanadan. Kazalika kuma, a wani taron da aka yi a birnin Rum, `yan kasar Kamaru dari 2 ne suka buya suka ki komawa kasarsu bayan an kammala taron. To irin wadannan dalilan ne dai ke sanya ofisoshin jakadancin Jamus din yin dari-dari wajen bai wa matasa daga nahiyar Afirkan biza.

Amma a ganin Christian Schärtl, na kungiyar matasan katolika ta nan Jamus, ofisoshin sun wuce gona da iri a matakan da suke dauka. A wata fira da na yi da shi, ya bayyana mini cewa:-

„A halin yanzu dai kasashen da wannan lamarin ya shafa sun hada ne da Togo, da Kamaru, da Senegal – wato kasashen da muke hulda da su. Game da Senegal ma, tun wannan batun bai taso ba ne muka fara huskantar matsala. A cikin watanni 3 da suka wuce, akwai wata tawaga da ta yi niyyar kawo ziyara a nan jihar Baveriya daga Senegal din, karkashin shirin musayar matasa da muke yi. Amma abin takaici, ziyarar ba ta yiwu ba, saboda mutum daya tak daga cikin mutane 6 da za su kawo ziyarar ne ya sami biza.“

To ko mene ne ke janyo irin wwadannan matsalolin da ake huskanta ?

A ganin Schärtl dai:-

„Matsalar da muke huskanta a Afirka Ta Yamma da kuma sauran wasu kasashen Afirka su ne, ban da dimbin yawan takardun da ake bukata daga matasan, kafin a ba su bizar, sai aka kuma kirkiro wani sabon salo na neman su kawo takardun inda suke aiki, da lambar ajiyar bankinsu da kuma takardun shaidar mallakar filaye ko kuma gidaje. Amma wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. Saboda duk matasan karkara da muke hulda da su, suna zaune ne da iyayensu, suna taya su aiki a gonakinsu. Sabili da haka, ba su da wasu kadarori na kansu da suka mallaka. Ta hakan ne kuwa, bisa wannan ka’idar, har abada ba za su taba samun biza ba.“