1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar rikicin filayen noma a Tanzaniya

Salissou Boukari
January 13, 2018

Mutane akalla 40 'yan sanda suka kama a kasar Tanzaniya bayan kashe wasu mutane guda biyu da aka yi a ranar Juma'a sakamakon wani tsohon rikicin filaye da ya hada gundumomi uku da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/2qoCv
Landwirtschaft Tansania
Hoto: DW/K. Makoye

Rikicin filayen dai ya shafi wajen heka 4000 na noma da ke kusa da babban gandun dajin nan na kasar da ke Serengeti, inda al'ummar yankin ke rikici kan filayen tare da gundumomin Bunda, Butiama, da kuma Serengetin wanda ko a watan Nuwamba da ya gabata, sai da wata tawaga ta gwamnatin kasar ta Tanzaniya ta je yankin domin neman magance rikicin.

A jiya Jumma'a ne dai rikicin da ya barke ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da aka kashe ta hanyar saransu da adduna yayin da suke aiki a cikin gonakinsu da ke cikin gundumar Serengeti, inda aka ce wadanda suka kai harin 'yan wani gari ne na gundumar Bunda a cewar Jarafi Mohamed shugaban 'yan sandan yankin, wanda ya tabbatar da kama mutanen 40 da ake zargi sannan ya ce suna ci gaba da neman wasu.