Matsalar Nakiyoyin Karkashin Kasa | Siyasa | DW | 19.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Nakiyoyin Karkashin Kasa

Har yau ana ci gaba da fuskantar barazana daga nakiyoyin da aka saba bibbinnewa a karkashin kasa a a sassa dabam-dabam na duniya

An saurara daga bakin Thomas Küchenmeister darektan wata kungiya mai adawa da nakiyoyin karkashin kasa yana mai fadin cewar a baya ga nakiyoyin da aka saba bibbinnewa karkashin kasa akwai wasu nakiyoyin masu hatsarin gaske wadanda ‚yan kanana ne da kan yi bindiga su tarwatse, kamar irin wadda ta rutsa da Wahid a garin Kerbala a kasar Iraki a lokacin da yake wasa da ita saboda yaro ne da bai san hadarinta ba. Nan take tayi bindiga ta fille hannunsa na dama ta kuma yi awon gaba da yatsunsa guda uku a hannunsa na hagu a baya ga raunuka masu yawa da ya samu a jikinsa. Wadannan nakiyoyi masu kama da harsasai da su kan barbazu ba tare da sun yi bindiga ba daidai suke da nakiyoyin da ake bibbinnewa karkashin kasa. Wadannan nakiyoyi tuni suka gurbata yankuna da dama da aka sha fama da yake-yake a cikinsu. A lokacin da yake bayani game da haka Küchenmeister karawa yayi da cewar:

Wadannan nakiyoyi masu tarwatsewa tuni suka zama kayar kifi a wuya a sassa dabam-dabam na duniya. A kasashe kimanin 25 aka yi amfani da wadannan nakiyoyi tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu abin da ya hada har da Irak da Kosovo da Afghanistan da kuma Sudan.

A Kosovo kadai mayaka na kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO sun yayyafa abin da ya kai harsasai masu tarwatsewa bayan sun yi bindiga har kimanin dubu 300 kuma har yau wadannan harsasai na ci gaba da gurgunta mutanen da tsautsayi kan rutsa da su a wannan yanki, Ya-Allah manoma ne ko mutanen dake fita shan iska ko kuma yara a filayen wasa. Gaba da ya alkaluma sun nuna barbazuwar dubban miliyoyin wadannan harsasai masu tarwatsewa a kasashe kusan 30. Kuma ana ci gaba da samun bunkasar cinikin wadannan harsasai. Ita kanta Jamus tana daya daga cikin kasashen dake cin kazamar riba daga cinikin wadannan harsasai a cewar Thomas Küchenmeister, wanda ya ce a baya ga haka rundunar sojan kasar na da adanin abin da ya kai harsasai akalla miliyan talatin. Abin da kungiyarsa ta sa gaba shi ne tabbatar da ganin cewar rundunar sojan ta Jamus ba ta yi amfani da su ba. Kuma gwamnati zata dauki nagartattun matakai domin haramta sarrafawa da cinikinsu a ketare. Zai dai dauki lokaci mai tsawo kafin yarjejeniyar Geneva ta haramta wadannan muggan makamai. Kimanin kungiyoyi masu zaman kansu guda 100 a sassa dabam-dabam na duniya ke fafutukar ganin an haramta nakiyoyin karkashin kasa da sauran nakiyoyi da harsasai da kan nakasa dan-Adam bayan samun shekaru da dama da lafawar kurar yaki.