Matsalar Manema Mafakar Siyasa A Nahiyar Turai | Siyasa | DW | 21.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Manema Mafakar Siyasa A Nahiyar Turai

Ministan cikin gida na Jamus Otto schily ya fuskanci kakkausan suka daga kungiyoyin kare hakkin manema mafakar siyasa dangane da shawararsa game da bude kafofin bitar takardun manema mafakar siyasar a kasashen arewacin Afurka domin hana makaurata tuttudowa zuwa nahiyar Turai

Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily

Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily

Akwai muhimman dalilan da suka sanya shuagabannin kasashen Kungiyar tarayyar turai suka ki amincewa da shawarar ta P/M Birtaniya Tony Blair. Domin kuwa kungiyar ba zata iya yin gaban kanta wajen gina sansanonin karbar ‚yan gudun hijira a kasashen arewacin Afurka ba tare da wata madogara ta doka ba. Bugu da kari kuma ku da yake ministan cikin gidan Jamus Otto Schily har yau ba ya goyan bayan gina ire-iren wadannan sansanoni, amma maganarsa a game da gina wuraren bitar takardun ‚yan gudun hijirar dake neman shigowa nahiyar Turai a kasashen na arewacin Afurka abu ne na damuwa. Domin kuwa ayar tambaya a nan shi ne ko shin ba yunkuri ne kasashen na Turai ke yi domin danka matsalar manema mafakar siyasar akan kasashe masu tasowa ba ta yadda nan gaba za a wayi gari nahiyar Turai bata da wata matsala ta ‚yan gudun hijira. A dai wannan marra da ake ciki duk wani da ya mika takardunsa na neman mafakar siyasa, Ya-Allah a nan Jamus ne ko wata kasa ta KTT, zai fuskanci zargin cewar kokari yake yi domin kyautata makomar rayuwarsu. Wato kaurarsa ba ta da wata nasaba da siyasa, ya shigo nahiyar Turai ne domin neman mafakar tattalin arziki. Shi kansa wannan zargin akan danganta shi da wata manufa ta miyagun laifuka. Tamkar dai makauratan kokari suke su mamaye guraben ayyukan yi ko kuma su dogara kacokam akan tattali na gwamnati domin kyautata makomar rayuwarsu ba a bisa ka'ada ba. Babu wani dake ba da la’akari da gaskiyar cewar galibi wadannan manema mafakar siyasa su kan karbi ayyuka ne wadanda Jamusawa ke kyamar aikata su, ko kuma masu dogaro akan tallafi daga gwamnati suna hakan ne saboda an haramta musu kama aiki. Jami’an siyasa ‚yan kalilan ne ke gabatar da kira tsakani da Allah a game da karbar ‚yan gudun hijira dangane da koma bayan da Jamus ke fama da shi ga yawan al’umarta. Amma hatta ita kanta sabuwar dokar kaka-gida da aka zayyana ba ta tanadi wannan manufa ba. A maimakon haka za a ci gaba ne da tankade da rairaya domin tace manema mafakar siyasar da ba a kaunar ganinsu a kasar daga wadanda ake ganin cewar sun yi hijira ne saboda dalilai na jinkai. Abin fata dai a nan shi ne shawarar ta Schily ta zama ra’ayi ne kawai da ba zai tabbata ba. Ire-iren wadannan ra’ayoyin ba zasu tsinana kome wajen shawo kan matsalar ta manema mafakar siyasa ba. Abu mafi alheri shi ne kasashen na Turai su nemi nagartattun hanyoyin kyautata manufar karbar manema mafakar siyasar a maimakon neman shingence nahiyar baki daya.