1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar man fetir ta ta'azzara a Najeriya

Uwais Abubakar IdrissDecember 21, 2015

A dai dai lokacin da ake shiga jajibirin hutu na bikin Krismati, karancin man fetir ya kara munana a sassa da dama na Najeriya tare da haifar da matsalolin zirga-zirga.

https://p.dw.com/p/1HRAY
Hoto: picture-alliance/ dpa

Matsalar karancin man da ta faro Kaman wasa sannu a hankali ta zama babban batu, domin lita mai da a bisa farashin gwamnati ake sayar da ita a kan Naira 87 a yanzu ta kai sama da Naira 250 a Abuja da ma wasu sassan Najeriyar. Wannan yanayi ya samar da kafa ga wasu ‘yan bumburutu a Abuja inda suke cin karansu ba babbaka. Matafiya da ke kai da komowa a cikin birane da ma masu tafiya zuwa wasu sassan Najeriyar ne dai abin yafi shafa, kamar yadda Shehu Dabo wani matafiyi yake bayani...

Nigeria Benzin Schwarzmarkt
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Owolabi

"Lallai matsalar karancin man nan ya shafi dukkanin harkokinmu na rayuwa bama na tafiye-tafiye ba, domin kudin da ka saba biya in zaka yi tafiya daga wannan unguwa zuwa wancan a Abuja abin ya canza sosai, kudin sun yi tsada, inda ka ke biyan Naira 100 yanzu sai ka biya 150 koma fiye da haka. In ka yi magana da direba sai yace maka ai matsalar mai ta kawo haka’’.

Ganin cewa mafi yawan gidajen mai na ‘yan kasuwa masu zaman kansu basu da man bayan kuwa gwamnati ta biya sama da Naira bilyan 400 a matsayin kudin tallafin ga masu shigo da man, har ma da karin da majalisar dattawa ta yi don kaucewa fuskantar matsala. Tuni dai ministan kasa a ma’aikatar man fetir din Najeriya Ibe Kachukwu ya bada umurni ga hukumar sashin kula da man fetir da ya rubanya yawan man da ake samarwa domin saukaka halin da ake ciki. Amma me yasa ake fuskantar wannan matsala duk da biyan kudin talafin da ma aikin da matataun man na Najeriya ke yi? Dr Ibe Kachukwu shine ministan kasa a ma’aikatar man fetir din Najeriyar.

Benzin Afrika
Hoto: picture-alliance/ dpa

‘’Halin da matatun man Najeriya ke ciki kamar yadda muka bayyana alkaluman watan Octoba basu samar da ko lita guda ba, kuma har zuwa yanzu nan basu aiki , amma dai mai yiwuwa nan da ‘yan kwanaki matatun man a Fatakwal da Kaduna za su fara dan aiki, amma gaskiyar lamarin shine halin matatun nan fa sai an kamala gyara tukuna. Ba zamu dogara a kan matatun man na Najeriya ba don samun man fetir a yanzu’’.

A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da dandana azabar karancin man fetir a kasar da take ta da arzikin mai a duniya a yanayi na ga koshi ga kwanan yunwa, kwararru na bayyana bukatar hanzarta gyaran matatun man ko gina wasu, muddin kasar na son shawo kan matsalar, domin kusan kashi 80 na man da ake sha a kasar a yanzu ana shigowa das hi ne daga kasashen waje ake.