Matsalar kyamar baki a Jamus | Siyasa | DW | 19.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar kyamar baki a Jamus

Tun bayan sake hadewar Jamus shekaru 16 da suka wuce ake fama da matsalar kyamar baki a kasar

Zanga-zangar adawa da kyamar baki a Potsdam

Zanga-zangar adawa da kyamar baki a Potsdam

Tun bayan sake hadewar Jamus shekaru 16 da suka wuce ake fama da matsalar wariyar jinsi da kyamar baki musamman a gabacin kasar. Rahotanni masu nasaba da ma’aikatar cikin gida ta jihar Brandenburg sun ce a shekarar da ta gabata an fuskanci hare-haren kyamar baki har sau 97 wadanda kuma suka shafi mutane daga kasashe daban-daban har 16 kuma kimanin kashi biyu bisa uku daga cikinsu suna rike ne da takardun fasfo na Jamus. Tun dai bayan sake hadewar a shekara ta 1990 jihar Brandenburg ta fara shiga kanun labarai dangane da tashe-tashen hankula na kyamar baki, inda a cikin watan nuwamba na shekarar ta 1990 wasu masu aski kamar kwaryar dake da zazzafan ra’ayi na wariyar launin fata suka kai hari tare da kisan wani dan kasar Angola Antonio Amadeo. A shekarar 1996 wasu matasa dake da irin wannan akidar sun shiga farautar wani bakar fata dan usulin Birtaniya Noel Martin da mota har sai da yayi hadari kuma wani bangare na jikinsa ya shanye. Kazalika a shekarar 1998 masu akidar kyamar baki da banbancin launin fata sun kai hari tare da ji wa wani dan kasar Gambiya mummunan rauni. Akwai dai alkaluma masu tarin yawa da aka tara, wadanda ke bayani game da ire-iren wannan ta’asa kuma farmakin da aka kai kan dan kasar Habashan a ranar lahadi da sanyin safiya shi ne na baya-bayan nan da aka sake fuskanta dangane da kyamar baki a jihar Brandunburg. To sai dai kuma magajin garin Potsdam Jann Jakobs ya nuna cewar a garin nasa babu wata takamaimiyar kungiyar da aka kafa mai akidar wariya da kyamar baki, inda yake cewar:

A Potsdam ba mu da angizon kungiyoyin kyamar baki. Wannan kuma shi ne abin da ya banbanta mu da sauran garuruwa kamar Berlin. Amma abin dake akwai shi ne ire-iren wadannan kungiyoyi suka shigo nan garin ne domin aikata ta’asarsu, ko da yake a daya bangaren akwai masu goya musu baya a fakaice. Amma mahukunta sun sa ido akan kai da komonsu.

Ayar tambaya a nan dai ita ce mene ne musabbabin wannan akida ta kyamar baki da banbancin launin fata dake addabar mazauna gabacin Jamus. Shin har yau basu fahimci manufar demokradiyya ba ne ko kuwa rashin sabo ne da cude-ni-in-cude-ka da sauran jinsunan mutane sakamakon halin da suka kasance a ciki bayan yakin duniya na biyu? Akwai dai masu ra’ayin cewar ita manufar ta wariya ba lalle ba ne ta kasance tana da nasaba da wata kungiya mai ra’ayin rikau. Abu ne da ya shafi wata akida dake zukatan mutane ko da yake idan ba a yi taka tsantsan ba sai ta kai su ga kirkiro wadannan kungiyoyi domin yayata akidarsu tsakanin jama’a. Akwai kuma masu danganta lamarin da matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a jihohin gabacin Jamus. Amma wani da ake kira Wolfgang Arnold daga kungiyar fafutukar tabbatar da mulkin demokradiyya da zaman hakuri da juna dake nan kasar ya ce a ganinsa wannan matsalar ba ita ce kadai ummal’aba’isin kyamar bakin da ake fama da ita a wadannan yankuna ba.

Ina tababa a game da cewar bunkasar tattalin arziki na da wata muhimmiyar rawar da zata taka domin gusar da wannan akida daga zukatan mutane. Ana iya samun bunkasar tattalin arziki ba tare da wata akida ta demokradiyya da zaman hakuri da juna ba. A saboda haka matsaloli na tattalin arziki ba zasu iya kasancewa sune kadai ummal’aba’isin wannan mummunar akida ba. Matsalar dake akwai ita ce ta sako-sako da gwamnati tayi da matakan wayar da kan matasa kuma a nan ne take kasa tana dabo.