1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

031111 Krisengipfel Cannes

November 3, 2011

Shin taron G20 zai iya dawwamar da Girka a matsayinta na ƙasa mai amfani da kuɗin Euro ? Sakamakon zaɓen raba gardama a ƙasar ta Girka game da yarjejeniyar tallafin da za ta samu zai ba da amsar wannan tambaya

https://p.dw.com/p/134mk
Shugabannin ƙasashen G20Hoto: dapd

Shugabannin ƙasashen mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a duniya wato G20 sun hallara ka'in da na'in a birnin Cannes na ƙasar Faransa domin duba hanyoyin samun mafita daga matsalar kuɗi da ke addabar duniya. To sai dai saɓanin yadda aka saba a wannan karo ajandar taro ta karkata ne akan shawarar da fraiministan Girka, George Papandreou ya tsayar ta gudanar da zaɓen raba gardama akan makomar ƙasar tsakanin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro.

Tasirin shawarar gudanar da zaɓen raba gardama

Taron dai ya fi mai da hankali ne akan sabon rikicin da ya taso a dangane da zaɓen raba gardama da Girka ta tsai da shawarar gudanarwa da kuma yadda sakamakon zaben zai kaya. Ko shakka babu shawarar da Girka ta tsayar ta gaban kanta ta haifar da wani ruɗani na daban a cewar Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus. Ta ce zaɓen raba gardamar dai na zaman abin da zai bayyanar da matsayin Girka tsakanin ƙasashe masu amfani da kuɗin euro.

Frankreich Deutschland G20 Gipfel in Cannes Angela Merkel
Angela MerkelHoto: dapd

" Muna son mu taimkaka wa Girka. Muna kuma son ta ci gaba da zama mamba ta ƙungiyar ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro. To amma hakan zai dogara ne akan shawarar da Girka kanta ta tsayar. A don haka muke cewa sai Girka ta amince da dukan abubuwan da shawarar da aka cimma a taron ƙungiyar Tarayyar Turai na ranar 27 ga watan Oktoba ta ƙunsa sannan mu biya kashi na shida na tallafin da take buƙata. Akwai kuma buƙatar sakamakon zaɓen ya kau da duk shakkun da ake yi ta yin amanna da kuɗin Euro . Mun dai yi bayani dalla-dalla. Babbar ayar tambaya anan dai ita ce shin Girka tana son ci gaba da amfani da kuɗin Euro ko kuma a'a.

Merkel ta ce in da so samu ne za su gwammace samar da mafita daga matsalar da kuɗin Euro ke tsintar kansa a ciki tare da Girka.

"Ana buƙatar ƙarfafa baki ɗayan kuɗin euro. Mun fi son cimma haka tare da Girka. To amma tabbatar da ɗorewar kuɗin Euro shine ne akin mafi muhimmaci da ya zamo wajibi mu aiwatar.

Ƙoƙarin Faransa wajen samun mafita

A nasa ɓangaren shugaba Nikolas Sarkozy na Faransa jadaddawa ya yi da cewa ana buƙatar martaba shawarar da Girka ta tsayar ta gudanar da zaɓen raba gardama game da yarjejeniyar da aka cimma domin ba ta tallafi a taron da ya gudana a birnin Brussels na ƙasar Beljiyam. Ya ƙara da cewa su kuma al'umar Girka suna buƙatar martaba dukan dokokin da ƙasashen Turai suka tsayar.

Shugaba Barack Obama na ƙasar Amirka da ke a matsayin abokiyar aiki ta Ƙungiyar Tarayyar Turai yabawa ya yi da irin namijin ƙoƙarin da shugaba Nikoas Sarkoy ke yi wajen tinkarar matsalar kuɗi da ke addabar duniya

"Ɓangare mai muhimmaci na aikin da ke a gabanmu cikin kwanaki biyu masu zuwa shine magance matsalar kuɗi da ke addabar Turai. Shugaba Nikolas Sarkozy ya nuna shugabanci na daban game da wannan al'amari . Na yarda da maganar da ya yi cewa Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ɗau wasu muhimman matakai domin samun kyakyawar mafita. In ba don Sakozy ba da ba a cimma hakan ba.To amma a nan wurin za mu tatance shirin da za a iya zartarwa a cikin tsanaki.

Taimakon ƙasashe masu samun ci gaba a cikin gaggawa

Hu Jintao und Barack Obama
Hu Jintao da Barack ObamaHoto: AP

Da yammacin Laraba 02-11-2011 ne kuma Shugaba Hu Jintao na China ya shiga tatunawa tare da Sarkozy domin duba yadda su kuma ƙasashe masu samun ci-gaban a cikin gaggawa za su iya ba da tasu gudunmuwa wajen tsamo kuɗin Euro daga matsalar da ya tsunduma. To sai dai waɗannan ƙasashen na buƙatar jira domin ganin ko ƙasashen Turai za su ci gaba da tafiya tare da Girka.

Za a iya sauraron sautin wannan rahoto daga ƙasa.

Mawallafi: Daniel Scheschkewitz/Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman