Matsalar kuɗi a ƙasar Girka | Siyasa | DW | 16.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar kuɗi a ƙasar Girka

Ƙasashen Turai masu amfani da Euro sun yanke shawara taimakawa Girka ta fita daga talaucin da ya mamaye ta.

default

Ƙasashe masu kuɗin Euro zasu taimakawa Girka ta fita daga talauci.

Ministocin kula da harkokin kuɗi na rukunin ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗi ta Euro, sun gudanar da taro a birnin Brussels na ƙasar Beljiam, inda suka bayyana yiwuwar taimakawa ƙasar Girka da rance  a ƙoƙarin da take yi na shawo kan matsalar bashin da ya yi mata ka'tutu.

Taron ministocin kula da harkokin kuɗi na rukunin ƙasashen Turai 16 dake yin amfani da Euro, wanda aka gudanar a ƙarƙashin jagorancin Frime Ministan Luxembourg Jean-Claude Junker, ya bayyana cewar, a shirye gungun ƙasashen suke su baiwa Girka rance - idan har buƙatar hakan ta taso, domin samar da daidaito a harkokin kuɗi na ƙasashen dake yin amfani da takardar Euro. Shugaban gungun ƙasashen, Jean-Claude Junker, ya ce ko da shike ya zuwa yanzu ƙasar ta Girka bata nemi wannan tallafin ba, amma ba zasu yi wata-wata ba, wajen kai mata ɗauki  da zarar ta buƙaci hakan: Mun tantance matakai na bai-ɗaya da zamu dogara da su, domin taimakawa Girka, idan buƙatar hakan ta taso.

Wata sanarwar da taron ministocin kuɗi na gamayyar ƙasashen dake amfani da Euron ta fitar, ta bayyana cewar, manufar bayar da rancen, ita ce bayar da kariya ga daidaiton sha'anin kuɗi a yankin ƙasashen, kuma sanarwar tace rukunin ƙasashen sun daddale hanyoyin da zasu bi wajen ɗaukar mataki na bai ɗaya - ta yadda hakan zai dace da yarjejeniya Tarayyar Turai, kamar yadda ministar kula da harkokin kuɗi a ƙasar Faransa, Christine Lagarde, wadda ita ma ta halarci taron ta sanar:

Wannan shirin, zai dace ne da yarjejeniyar Tarayyar Turai, da kuma dokokin da ƙasashen dake cikin shirin ke yin aiki da su, kana kuma majalisar Tarayyar Turai zata iya hanzarta ɗaukar mataki akan batun.

Ƙasar ta Girka dai, na fafutukar warware bashin dake kanta na kuɗi Euro miliyan dubu 300, wato kwatankwacin dalar Amirka miliyan dubu 410, kuma hatta a yanzunnan da ake magana, tana buƙatar kimanin kuɗi Euro miliyan dubu 54, ko kuma dalar Amirka miliyan dubu 70  - a bana kawai, domin biyan wannan bashin - lamarin daya sanya gwamnatin ƙasar ɗaukar matakai daban-daban, wanda a sakamakon hakan kuma ta fuskanci zanga-zanga daga ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, waɗanda suka ce matakan sun yi tsauri - ainun.

A yanzu dai taron shugabannin ƙungiyar Tarayyar Turai, mai ƙasashe mambobi 27 da za'a gudanar cikin makon gobe idan Allah ya kaimu ne zai bayar da umarnin miƙawa ita Girka wannan rancen, bisa la'akari ga dacewar hakan.

A cewar kwamishinan kula da harkokin kuɗi dana tattalin arziƙi na ƙungiyar tarayyar Turai Olli Rehn, taron ministocin ya yi amannar cewar Girka na bisa kyakkyawar turbar aiwatar da manufofin da zasu inganta tattalin arziƙinta idan aka dubi sauye sauyen da take samarwa, kuma ƙungiyar tarayyar Turai ma ta yi na'am da hakan:

Gwamnatin Girka ta yanke muhimmiyar shawarar gabatar da wani ƙasaitaccen shiri, da kuma ɗaukar ƙarin matakai, wanda ke nufin ƙasar na bisa sahihiyar hanyar cimma burin rage giɓin kasafin kuɗinta da kashi huɗu cikin 100 a wannan shekarar. Lallai wannan muhimmin mataki ne ta fuskar daidaita tafiyar da harkokin kuɗi ga al'ummar Girka.

Ana sa ran sabbin matakan da ake ɗauka zasu taimakawa ƙasar Girka shawo kan ƙangin talaucin data faɗa cikinsa.

Mawwallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou Madobi