1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar karuwar Yara Marayun AIDS a nahiyar Afirka.

Mohammad Nasiru AwalNovember 27, 2003
https://p.dw.com/p/BvnP
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF da kuma hukumar kula da cutar AIDS ta MDD wato UNAIDS a takaice sun yi kira ga kasashen Afirka da su kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba don taimakawa marayu da cutar AIDS ko SIDA ta halaka iyayensu. Alkalumman da hukumomin biyu suka bayar sun yi nuni da cewa kimanin kashi 4 cikin 5 na yara marayu da AIDS ta kashe iyayensu, wato marayun AIDS kamar yadda ake kiransu yanzu, a Afirka suke. A wani taron manema labarai da suka yi a birnin Johannesburg na kasar ATK, shugabar asusun UNICEF Carol Bellamy da mataimakiyar daraktan hukumar UNAIDS Kathleen Cravero da kuma Graca Machel uwargidan tsohon shugaban ATK Nelson Mandela, sun yi kira ga kasashen Afirka da su bullo da wani gagarumin shirin taimakawa irin wadannan yara. Wani rahoton da asusun UNICEF ya bayar yayi nuni da cewa a Afirka, nahiyar da ta fi ko-wace a duniya fama da matsalolin AIDS, yanzu haka akwai yara marayu na AIDS da suka kai miliyan 11, kuma har yanzu babu wani nagartaccen shirin magance wannan matsala. Kwararrun masana sun yi nuni da cewa idan ba´a gaggauta daukar matakan tinkarar wannan matsala, to yawan kananan yara dake rasa iyayensu sakamakon cutar AIDS a Afitrka zai kai miliyan 20 kafin shekara ta 2010.
Babbar daraktan asusun Carol Bellamy ta ce kyakkyawan tsarin taimakawa marayu bisa al´adar Afirka yanzu ya na fuskantar barazanar rugujewa saboda yawan marayu da ake dada samu, musamman sakamakon cutar AIDS. Misis Bellamy ta ce wannan wani mummunan bala´i da zai kassara nahiyar Afirka a lokaci mai tsawo, face gwamnatoci da gamaiyar kasa da kasa sun kai dauki. Alkalumman da aka bayar sun yi nuni da cewa yawan wadanda suka kamu da kwayoyin HIV ko Cutar Aids a kasashen Afirka kudu da Sahara sun kai miliyan 26.6. Masu bincike na cutar AIDS sun ce dalilan da ke sa wannan cuta ke yaduwa kamar wutar daji a Afirka shine sau da yawa masu alaka ko kuma bin mata masu zaman kansu, ba sa daukar wani mataki na kare kansu daga kamuwa da wannan cuta. Haka zalika gwamnatocin Afirka kansu ba sa daukar yaduwar cutar da wani muhimmanci, musamman idan aka yi la´akari da cewa kashi 2 cikin 3 na gwamnatocin kasashen kudu da Sahara ba su da wani shiri na kare al´umarsu daga cutar AIDS. Asusun UNICEF ya ce a kasashen Afirka ma da a halin yanzu akan dan yi nasarar magance yaduwar wannan cuta kamar Uganda, ka iya fuskantar matsalar karuwar marayu, domin ana kara samun iyaye dake mutuwa sakamakon cutar ta AIDS. UNICEF yayi kira da a ba da taimakon gaggawa don marawa shirin ilimantarwa tare da jiyyar wadanda suka kamu da cutar ta AIDS.