Matsalar karancin abinci a Senegal | Siyasa | DW | 11.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar karancin abinci a Senegal

Akwai matsalar karancin abinci mai gina jiki ga yara a kasar Senegal

A kokarin tinkarar wannan matsala ta karancin sinadari mai gina jiki asusun UNICEF a hadin guiwa da kungiyar taimakon abinci ta MDD ya bude wata cibiyar ba da taimakon wasu kwayoyi masu sinadarin vitamin A da bude wurarin cin abinci a makarantu a kasar ta Senegal. To sai dai kuma dauruwan uwayen yara kan yi tafiya ta tsawon sama da kilomita 100 domin halartar wannan cibiya. A yayinda ubannin yaran kan koma bakin ayyukansu, su kuma uwayen yaran sai su kwana a cibiyar tare da ‘ya’yansu. To sai dai kuma cibiyar tana fama da matsala sakamakon dimbim majiyyata dake hallara don neman magani saboda duka-duka gadaje 24 ne take da su. Du, wanda ya leka farfajiyar cibiyar zai yi zaton wani sansani ne na ‘yan gudun hijira..A lokacin da take bayani dangane da matsalar karancin abinci ga yara wata Nes mai suna Regina cewa tayi:

“A hakika bai kamata a ce jarirai na fama da karancin abinci ba. Duk matar da zata yi tsawon wata shida tana shayar da jaririnta wajibi ne ta tabbatar da cewar ya samu isasshen abinci. Amma daya matsalar da ake fama da ita a nan kasar ita ce ta mace-macen uwayen yara fiye da kima. Wato muna fama da marayu masu tarin yawa. A baya ga haka wasu daga cikin uwayen suna da ‘yan biyu ko uku ta yadda basu da ikon bai wa jariran nasu isasshen abinci domin kare makomar lafiyarsu.”

Amma fa a baya ga wadannan matsalolin akwai kuma wasu dabam da Regina da sauran ma’aikata na cibiyoyi 15 da aka kafa a duk fadin kasar Senegal ke fama da su, wadanda musamman suka shafi nau’in abinci da ya kamata a ba wa yaro ko jariri. Regina dai ta ci gaba da cewar:

“Yawancin uwayen yara, wadanda basu da karatu, ba su san cewar ana iya bai wa yaro nama ko da bai fara fid da hakori ba. Tana iya ninnike naman ta yadda yaron zai samu sinadarin da yake bukata daga dabba. Wannan maganar ta shafu har da kwayaye. Misali akwai masu camfin cewar yaron da bai fara tafiya ba bai kamata a rika ba shi kwai ba, wai saboda hakan zai sanya ya tashi ta sace-sace ko kuma ba zai iya magana ba, wato zai zama bebe. Wadannan camfe-camfe na taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar makomar jin dadin rayuwar yara.