Matsalar Kanjamau A Afurka | Siyasa | DW | 01.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Kanjamau A Afurka

Ba kasafai ba ne ake ba da la'akari da yara kanana a game da maganin cutar kanjamau

Kanjamau a Afurka

Kanjamau a Afurka

Galibi dai an yi watsi ne da makomar yara a matakan da ake dauka domin tinkarar cutar kanjamau, ko kuma Aids a turance. Yawan yara masu kamuwa da kwayar cutar sai dada karuwa yake kuma kimanin kashi tara bisa goma na yaran dake da kwayar cutar a nahiyar Afurka suke. Kazalika bayanai sun nuna cewar kashi daya daga cikin shida na wadanda ke mutuwa sakamakon cutar kanjamau yara ne kanana. Sai daga baya-bayan nan ne kamfanonin harhada magunguna suka fara sarrafa magunguna don amfanin yara masu kwayar wannan cuta. Amma yawan kasashe masu tasowa dake da ikon sayan magungunan bai taka kara ya karya ba. Misali a kasar Afurka ta Kudu yara dubu biyar ne kacal suka samun jiyyar cutar daga cikin yara dubu 50 dake bukatar magani a kasar. Ita kanta kasar Lesotho, wadda ita ce ta uku a cikin jerin kasashen da cutar tafi yaduwa a cikinsu a cikin hamzari, sai a baya-bayan nan ne ta fara gabatarwa da yara maganin cutar. Dagmar Wittek, wakiliyar DW ta kai ziyara wani karamin asibitin jiyyar Kanjamau dake Tsepong a lardin Leribe na kasar Lesotho inda ta sadu da wata mai suna Manyane Motobile, wadda ita da mijinta da kuma ‚yarsu mai shekaru shida da haifuwa ke neman magani a wannan asibiti. A lokacin da aka tambayi albarkacin bakinta Manyane Motobile cewa tayi:

Mijina kann fada mini cewar ka da ki kuskura ki fada wa yaran kome. Babu daya daga cikin danginmu dake da wata masaniya a game da cewar muna dauke da kwayar cutar. Daga ni sai shi sai kuma wani dan-uwana, wanda malamin kiwon lafiya ne a asibiti.

A cikin watan mayun da ya wuce ne Manyane ta samu bayanin cewar ita da mijinta da kuma karamar ‚yarsu mai shekaru shida da haifuwa na da kwayar cutar ta kanjamau. Mijinta dan ci-rani ne a Afurka ta Kudu kuma ba ya kai ziyara gida sai jefi-jefi, har sai bayan da ya kamu da cutar yake kuma kwance rai hannun Allah. Manyane ta shawo kann mijin nata domin a gwada jininsu da kuma na ‚yar tasu saboda tun bayan haifuwarta take fama da rashin koshin lafiya. Bayan da aka gwada jinin ne likitoci suka tabbatar da cewar dukkansu uku na dauke da kwayar HIV. A yanzun dai yarinyar mai suna Tabello ta fara nuna kazar-kazar inda ta kann kalli telebijin take kuma wasa ta takwarorinta tun bayan da aka fara yi mata jiyya da wani maganin dake taimakawa wajen farfado da kariyar jikinta. Wata likita mai suna Limpho Lekena dake karamin asibitin na jiyyar kanjamau ta ce babban kuskuren da aka caba da farko shi ne zaton da aka yi cewar ita cutar kanjamau cuta ce ta manya kuma ba ta shafi yara kanana ba. A halin yanzu haka yara 250 ne ke neman magani a wannan karamin asibiti dake lardin Leribe na kasar Lesotho, wadda kamar yadda muka fada, duk da kankantarta, amma ita ce ta uku daga cikin jerin kasashen da cutar ta fi yaduwa a cikinsu a cikin hamzari.