Matsalar jigilar Jiragen sama a nahiyar Turai | Labarai | DW | 19.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar jigilar Jiragen sama a nahiyar Turai

Ministocin sufuri na ƙasashen Turai zasu yi nazarin matsalar da sufurin jiragen sama ke ci gaba da fuskanta a yankin

default

Zirga - zirgar jiragen sama a nahiyar Turai zata ci gaba da fuskantar matsala har ya zuwa yau Litinin, a yayin da gajimaren toka daga wani dutsen dake aman wuta a ƙasar Iceland ke ci gaba da shafar nahiyar. A jiya Lahadi dai an sami wasu jirage - 'yan ƙalilan da suka tashi a filayen sauka da tashin jiragen Sama na Jamus, amma yanzu kuma ɗaukacin jiragen suna ƙasa - har ya zuwa ƙarfe biyu na rana agogon Jamus. Kimanin ƙasashe 30 ne ke ci gaba da ko dai rufe filayen su ko kuma taƙaita zirga - zirgar jiragen sama domin fargabar kare lafiyar fasinjoji - lamarin daya jefa kimanin fasinjoji miliyan bakwai a duniya cikin rashin tabbas na lokacin tafiyar su.

A halin da ake ciki kuma, a yau Litinin ne ƙasar Spain, wadda ke riƙe da shugabancin ƙungiyar tarayyar Turai ta ƙira taron gaggawa ta na'urar bidiyo na ministocin kula da harkokin sufuri a ƙasashen yankin, domin yin nazarin halin da ake ciki. Tunda farko dai, sakataren kula da harkokin tarayyar Turai a Spain, ya sanar da cewar, akwai yiwuwar yau Litinin, rabin jiragen dake jigila a nahiyar Turai zasu koma ga ayyukan su.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Mohammad Abubakar