1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar hada-hadar muggan ƙwayoyi a Guinea Bissau

Ƙasashen Duniya sunyi alƙawarin tallafawa ƙasar Guinea Bissau da Dolar Amirka miliyan shida da ɗigo bakwai. Za a yi amfani da kuɗaɗen ne, wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi ne a ƙasar. An dai yi alƙawarin tara waɗannan kuɗade ne, a wani taro na wuni ɗaya daya gudana a birnin Lisbon na ƙasar Portugal. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Jami´in diplomasiyya na Majalisar Ɗinkin Duniya, Mr Shola Omoregie, na jaddada muhimmancin wannan shiri. A baya Faraministan Guinea Bissau, Martinho Dafa Cabi ya bayyana gazawar ƙasar, wajen yaƙi da ma su hada-hada da kuma safarar ƙwayoyin a ƙasar. Hakan a cewar Faraministan nada nasaba ne da talauci da kuma rashin tsaro dake addabar wannan ƙasa. Rahotanni dai sun ce Guinea Bissau ta kasance zango ne da ake hada-hada da kuma jigilar ƙwayoyi ne daga Afrika izuwa Nahiyar Turai.