1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MATSALAR HABAKAR FATAUCIN YARA KANANA A DUNIYA.

Yahaya Ahmed.November 19, 2003
https://p.dw.com/p/BvnZ
Fataucin yara a duniya sai kara habaka yake yi, inji Majalisar dinkin Duniya. Asusun Taimakon Yara na Majalisar, wato UNICEF ya kiyasci cewa a ko wace shekara, kusan yara miliyan daya da digo 2 ne ake fataucinsu a duniya baki daya, wasu a tilasa musu yin aikin dole kamar bayi, wasu kuma a sa su karuwanci. Alkaluma dai na nuna cewa, ban da harkokin miyagun kwayoyi da sumogan makamai, fataucin yara kanana ne hanyar da wasu kungiyoyin `yan marasa imani ke bi don azurta kansu. Amma ba a kasashe matalauta ne kawai ake samun ire-iren wadannan illolin ba. A kasashen kungiyar Hadin Kan Turai ma, ana samun habakar fataucin yara kanana.

Dalilan hakan kuwa na da yawa: Da farko dai salon nan na Globalisation, ko kuma hadayyar tattalin arzikin duniya, ya janyo wata bukata ta leburori, masu araha, ko kuma wadanda ba a biyansu wani albashin kirki. Ta hakan ne kuwa, a ko wace shekara, ake fataucin yara kanana, maza da mata, kimanin dubu dari da 20, daga yankin gabashi zuwa yammacin Turai, inji kiyasin da Hukumar UNICEF ta yi. Kamar dai yadda Ferdinando Imposimato, wani jojin kasar Italiya, mai bai wa Majalisar dinkin Duniya shawara kan fataucin mutane ya bayyanar, matsalar ta fi yadda ake zato muni:

"Fatauci da mutane, musamman ma dai yara, sai kara habaka yake yi, yana kuma zamowa harkar kasa da kasa. Ba kasashe daidai abin ya shafa ba kuma. Sabili da haka, ya kamata a kirkiro dabaru na kasa da kasa don yakan masu aikata wadannan laifuffukan a kasashen asali, da wadanda ake bi cikinsu da kuma inda ake kai yaran. Ana bukatar hadin kan duk kasashe, don hana yaduwar fatauci da mutane." kungiyar tallafa wa yaran nan Terre des Hommes, ta ce a ko wace shekara kusan yara miliyan daya ake fataucinsu a duniya. Ana amfani da su kamar leburori masu araha wajen sarrafa darduma, da tilasa musu yin aiki a wuraren samad da duwatsun gine-gine, ko a gonaki ko kuma dai a cikin gidajen masu kudi. Wasu yaran kuma, musamman mam dai mata, ana sa su ne yin karruwanci a kan dole, bayan an kai su wurare masu nisa da mahaifansu.

A nan Jamus ma, akwai yaran da ake shigowa da su ta hanyar boye, inda a karshe, idan mata ne, bayan an yi lalata da su, ake tilasa musu shiga wasu miyagun ayyuka kamarsu sai da miyagun kwayoyi, ko karuwanci ko kuma sata.

Fataucin yara dai, yana da jibinta da masu kasuwancin miyagun kwayoyi da `yan sumogan makamai. A kasashe da yawa kuma, cin hanci da rashawa, ya sa ba a iya fatattakar masu aikata wannan danyen aikin kamar yadda ya kamata, inji joji Imposimato. A nan Turai dai fataucin ya fi habaka ne a kasashen Rasha da Albeniya. Daga nan ne aka fi shigo da yara kanana zuwa yammacin Turai. Mafi yawan Rashawa da Albaniyawa masu wannan harkar, suna yin amfani da hanyar sadaswar nan ta Internet. Sabili da haka ne kuwa suke iya ma tallatad da kayan fataucinsu, wato yara, ba tare da jami'an tsaro sun san abin da ake ciki ba.

Kafin dai a iya shawo kan wannan matsalar, sai an kago wata sabuwar dabara ta bin diddigin masu tallata yara ta hanyar Internet din. Ferdinando Imposimato, ya bayyana ra'ayin cewa:

"Dole ne mu dau duk matakan ganin cewa, an zartad da dokoki wadanda ke da angizo a duk duniya baki daya, don hana fataucin mutane. Ya kamata kuma mu fadakad da jama'a don wayar musu kai game da illolin da fataucin mutane ke janyo wa al'ummomi. Kasashen da ba su da halin yakan wadannan miygun ayyukan kuma, kamata ya yi mu ba su duk taimakon da suke bukata. A nan Turai kuwa, tilas ne mu karfafa ayyukan hadin gwiwa don kau da wannan illar dindindin."