1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar Girka da Ƙungiyar Tarayyar Turai

March 2, 2010

Ana ci gaba da fama da neman hanyoyin ceton ƙasar Girka daga mawuyacin hali na taɓarɓarewar tattalin arziƙin dake barazana ga makomar darajar takardun kuɗi na Euro

https://p.dw.com/p/MHzz
Yajin aiki a Girka don adawa da matakan gwamnati na gyara tattalin arziƙin ƙasarHoto: picture alliance/dpa

Bayan ziyara da kwammishinar kula da tatalin arziki ta ƙungiyar tarayya turai ta kai a ƙasar ta Girka domin tautana tsarin da za a bi na tatalin arzƙi domin fitar da ƙasar daga cikin halin da take a yanzun.

Griechenland Finanzkrise Ministerpräsident George Papandreou
Piraminista Papandreou na ƙasar Girka dake fama da matsalar kuɗiHoto: AP

Nan gaba ne ran juma'a aka shirya shugabar gwamnatin ƙasar Jamus Angela Merkel zata sadu da firaministan ƙasar ta Girka George Papandreou abinda masu lura da al amuran yau da kullum ke kallon wani yunƙuri ne na musamun da zai kai ga samun taimako ga ƙasar Girka daga ƙungiyar Tarayya Turai.

Ko da shi ke tun can da farko an samu saɓani tsakanin 'yan jamiyyar FDP a cikin gwamnatin haɗin guiwa ƙasar Jamus wajen bayer da taimakon ga ƙasar Girka.

To amma ministan harakokin waje na ƙasar ta Jamus Guido Westerwelle ya bayyana cewa kafin duk a shiga wata tataunawa za mu so mu san abinda ƙasar ta Girka ta tanada na tsarin ta da komaɗar tatalin arziƙinta.

A gobe ne dai gwamnatin ƙasar ta Girka ta kira wani taron majalisar ministocin da zai ɗauki muhman shawarawari akan hanyoyin inganta tatalin arzikin ƙasar.

Wani kakakin Ƙungiyar Tarayyar Turai da ta kira taron manema labarai a yau a birnin Athens ya ce sun gamsu ƙwarai da aniya da matakai da ƙasar ta Girka ta tanada,

ya ce kuma gwanatin ta Girka a shirye take ta cimma manufofin da ta sa ma gaba domin cike giɓin da take da shi na kasafin kuɗin ƙasar da ya kai kashi takwas da rara cikin ɗari na jumullar abin da take samarwa a shekara.

To sai dai a halin da ake ciki a wani sakamakon bincike da Kungiyar Transparency International reshen ƙasar ta Girka ta fitar ya nuna cewa ƙasar na fama da matsalar cin hanci matuƙa duk da irin matsalar da take fama da ita akan harkokin tatalin arziƙi.

Reshen ƙungiyar na Trasnparency International a ƙasar Girka ya bayyana sakamakon ne bayan binciken da ya gudanar na ƙididiga akan al'amura daban daban wanda aka yiwa jama'ar ƙasar tambayoyi akansu.

A ciki mutane dubu shidda wanda aka riƙa yiwa tambayoyi na samun amsa kan cewa ko an taɓa karɓar kuɗi garesu ko yan uwansu domin cimma wata bukata ta gayra takardu ko a cikin ma'aikatu mallakar gwamnatin ko kuma a cikin kanfanoni masu zaman kansu.

Sakamakon ya nuna cewa kishi ashirin da takwas cikin ɗari na mutanen da aka yiwa tambayoyin sun amsa cewa tabbas an taɓa karɓar kuɗi a hannusu domin samun wata takarda da gaggawa ko kuma wani biyan bukata a bariki.

Ƙungiyar ta Transparency ta ce a shekara ta 2008 kusan million 750 na Euro aka karɓa daga jama'a na cin hanci abinda ya ɗara na shekara ta 2007 da million 110

Yayin da a shekara ta 2009 aka yi lisafin kuɗaɗe jumullar millions 787 na euro wanda aka kasasu kamar haka

millions 462 a karɓesu ne tamkar cin hanci a cikin maaikatu gwamnati sanan sai millions 325 a cikin kanfanonin masu zaman kansu

Rahoton dai ya nuna cewa an fi samun cin hancin ne a cikin Bankuna asibitoci da sauran maaikatu na gwamnatin,inda aka bada misalin cewa a asibiti an iya ƙiesta daga Euro 50 zuwa 600da akan iya karɓa na cin hanci.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane

Edita: Ahmad Tijani Lawal