Matsalar Cin Hanci A Afirka | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.10.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Matsalar Cin Hanci A Afirka

Matsalar cin hanci ita ce ummal'aba'isin koma bayan al'amuran rayuwa a Afirka

default

Marwa El-Sherbini

Ko da yake a wannan makon shari'ar Marwa El-Sherbini, Musulma 'yar ƙasar Masar da aka yi wa kisan gilla a wata kotu ta gabashin Jamus watan yulin da ya wuce, ita ce ta fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma duk da haka sun gabatar da rahotanni da dama akan al'amuran Afurka, musamman ma kan matsalar nan ta cin hanci da almundahana, waɗanda su ne ainihin ummal'aba'isin koma bayan da ƙasashen Afurka ke fama da shi. A cikin nata sharhin jaridar Der Freitag cewa tayi:

"A halin yanzu mutane sun fara ƙosawa da iƙirarin da aka sha yi musu na cewar mulkin mallaka da sabon salo na mulkin mallakan su ne musabbabin koma bayan ƙasashen Afirka ko kuma aƙalla har yau suna fama ne da tasirin wannan manufa. Amma fa wannan hujjar ana gabatar da ita ne a ƙoƙarin fakewa da guzuma domin a harbi karsana. Domin kuwa ainihin dalilin shi ne cin hanci da almubazzaranci da ƙwaɗayin tara abin duniya su ne ainihin tushen matsalar ta koma bayan al'amuran rayuwa. Alƙaluma da ita kanta ƙungiyar tarayyar Afirka ta bayar sun nuna cewar a sakamakon cin hanci da almubazzaranci nahiyar kan yi asarar abin da ya kai dalar Amirka miliyan dubu 140 a duk shekara. A saboda haka lokaci yayi da za a yi gayara ga lamarin a maimakon neman ɗora wa wasu laifi."

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tuntuɓar shugaban ƙasar Liberiya Ellen Johnson-Sirleaf tayi domin jin ta bakinta a game da taimakon raya ƙasa da makomar demoƙraɗiya a ƙasashen Afirka. Jaridar ta ce:

Ellen Johnson-Sirleaf Präsidentin Liberia

Shugabar Liberiya Ellen Johnson-Sirleaf

"Bisa ga ra'ayin shugabar ƙasar Liberiya dai tilas ne a samu haƙuri a game da mulkin demoƙraɗiyya a nahiyar Afirka. Saboda maganar abinci ita ce ta fi ci wa al'umar nahiyar tuwo a ƙwarya. Jama'a ba zata iya shiga a dama da ita a harkar demoƙraɗiya ba sai ta samu isasshen abinci da ruwan sha mai tsafta da nagartacciyar hanyar kiwon lafiya da ilimi da sauran abubuwan jin daɗin rayuwa ta yau da kullum. Kuma waɗannan abubuwan su ne Liberiya ta mayar da hankali kansu wajen aiwatar da kuɗaɗen taimakon da take samu, inda bana aka yi mata alƙawarin taimakon kuɗi na dalar Amirka miliyan 500."

A ƙarshen makon da ya gabata an sake fuskantar matsalar 'yan gudun hijira kimanin 300, waɗanda suka shafe sa'o'i aƙalla 72 suna watangaririya kan tekun bahar-rum tsakanin Libiya, Italiya da Malta a cikin wani ɗan ƙaramin kwale-kwalen da tsawonsa bai wuce mita 17 ba. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

500 Flüchtlinge im Mittelmeer vermisst

Kwale-kwale ɗauke da 'yan gudun hijira a tekun bahar-rum

"A tsakanin 'yan gudun hijirar, waɗanda akasarinsu 'yan Somaliya ne da Eritrea akwai mata 46, waɗanda huɗu daga cikinsu ke da juna biyu da kuma yara 'yan ƙanana 29. Ɗaya daga cikin 'yan gudun hijirar dai ya mutu kafin a kai musu ɗoki. Kuma bisa ga dukkan alamu mahukuntan Italiya na shirye-shiryen mayar dasu zuwa Libiya nan take, in banda 'yan gudun hijira daga Somaliya da Eritrea, waɗanda ke da haƙƙin samun mafaka bisa wata manufa ta jinƙai."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu