Matsalar Bakin Haure A Jamus | Siyasa | DW | 30.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Bakin Haure A Jamus

Kimanin mutane miliyan daya daga kasashen ketare ne suke zaune a nan Jamus ba a bisa ka'ida ba kuma kamfanoni da dama a kasar kan yi amfani da wannan dama domin ci da guminsu. A sakamakon haka mujami'ar Katolika take bakin kokarinta wajen ganin jami'an siyasa sun dauki nagartattun matakai domin kawo karshen wannan ci gaba

Akwai bangarori da dama na tattalin arzikin kasar nan kamar dai kamfanoni masu matsakaicin girma da na gine-gine da gidajen abinci da ayyukan noma dake ci da gumin wadannan bakin haure, wadanda aka kiyasce yawansu zai kai dubu 500 ko miliyan daya a nan kasar ta Jamus, kamar yadda aka ji daga bakin Peter Neher, shugaban gamayyar kungiyoyin taimakon jinkai ta Jamus. A saboda gudun ka da bacin rana ta rutsa da su a komar da su gida, wadannan bakin haure kan yi bakin kokarinsu wajen bar da kama. Yawa-yawanci su kan cimma nasarar haka, sai dai fa idan kaddara ta rutsa da mutum ya samu hatsari ko rashin lafiya, ko kuma juna biyu dangane da mata. A ire-iren wannan matsala mujami’ar Katolika kan ba da taimako iya mustada’a, saboda tilas tayi sara tare da duban bakin gatari, domin irin wannan taimakon ya saba wa tsarin doka. Ita dai gwamnati tana da cikakken ikon bin diddigin bakin haure da kuma fatattakarsu daga kasar, amma fa a daya hannun wajibi ne a mutunta dan-Adam daidai yadda ya kamata, lamarin da ya hada har da kula da makomar lafiyarsa ko da kuwa yana zama ne a kasar ba a bisa ka’ida ba, wannan shi ne abin da daftarin tsarin mulkin Jamus ya tanada, a cewar wani fada daga mujami’ar Katolika. Kowa na da hakkin samun muhallin zama da kula da kiwon lafiyarsa in ji Fada Alt, wanda ya kara da bayanin cewa:

Babu wata matsala ta karancin likitoci masu ba da hadin kai bisa manufa, amma a inda matsalar take shi ne kudaden da ake bukata na sayen magunguna da jiyyar marar lafiya ta dogon lokaci. Da yawa daga bakin hauren dake neman taimako daga wajenmu mata ne masu juna biyu dake kuma tunanin zub da cikin saboda matsalar kudi. Wadannan matsalolin sun dada yin tsamari a cikin shekarun baya-bayan nan.

A halin yanzu mujami’ar Katolika ta tsayar da shawarar gabatar da kira ga ‚yan siyasa domin su nemi bakin zaren warware matsalar ta bakin haure ta yadda zasu iya zama a cikin mutunci da kuma wata kafa ta kare kansu daga masu fafutukar ci da guminsu a nan kasar ta Jamus. Akwai mata da dama da akan tilasta musu shiga karuwanci kuma da wuya suke da ikon fid da kansu daga wannan mawuyacin hali na kaka-nika-yi. Kawo yanzun dai babu wata jam’iyya ta siyasa dake ba da la’akari da wannan batu in banda jam’iyyar nan ta The Greens, amma abin mamaki tana fuskantar mummunar adawa daga jam’iyyun Christian Union akan wannan manufa.