Matsalar Aikin Sojan Yara | Siyasa | DW | 17.11.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Aikin Sojan Yara

Dubban daruruwan yara ake tilasta musu shiga soja a sassan da ake fama da yake-yake a cikinsu

A halin da ake ciki yanzu haka akwai sojoji ‚yan kananan yara da ake fafatawa da su a yake-yake kamar a Afghanistan da Angola da Rasha da Uganda da wasu kasashe kimanin 20 a sassa dabam-dabam na duniya. Alkaluma sun nuna cewar a yankunan rikici na nahiyar Afurka, kamar Cote d’Ivoire da Burundi da Somaliya, adadin yaran dake cikin damarar yakin ya kai dubu 100. Kuma ko da yake duniya gaba daya ke Allah waddai da wannan ci gaba, amma har yau ana ci gaba da amfani da yara da kuma matasa, ba ma kawai a sojoji na gwamnati ba har da ‚yan sa kai da ‚yan tawaye. A lokacin da take bayani Victoria Forbes Adam daga kungiyar kasa da kasa mai adawa da aikin sojan yara ta ce da yawa daga cikin gwamnatocin dake da hannu a wadannan rikice-rikice suna amfani ne da ‚yan ta kife da dakarun sa kai ta yadda ba za a iya zarginsu da tilasta aikin soja akan kananan yara ba. A wasu kasashen ma sace yaran ake yi domin tilasta musu damarar makamai. Misali a farkon rikicin kasar Sudan dukkan gwamnati da ‚yan tawaye sun sha sace yara domin tilasta musu aikin soja. Akwai kuma yaran da dama, wadanda kan shiga sojan bisa radin kasu saboda ba su da wani zabi. Galibi zaka tarar su kansu sun fuskanci gallazawa da rashin adalci kuma a saboda haka sai su ci alwashin daukar fansa. Ta la’akari da haka ya zama wajibi a gabatar da nagartattun matakai na riga kafi a wannan bangaren in ji Victoria Frobes Adam. Ta ce babban abin da rahoton kungiyar tasu ya fi mayar da hankali kansa shi ne yadda za a shawo kan gwamnatoci da al’umar kasa baki daya a game da ba da cikakkiyar kariya ga yara ta yadda ba zasu wayi gari ba su da zabi illa su shiga aikin soja ba. Yarjejeniyar kasa da kasa domin kare makomar yara wani mataki ne na farko akan wannan manufa. Sai dai abin da ya rage shi ne a aiwatar da yarjejeniyar daidai yadda ya kamata. Ita ma kungiyar tarayyar Turai da MDD wajibi ne akansu su kara karfafa matakansu na kwance damarar yara kanana. Tilas ne a yi amfani da karfin hatsi wajen dakatar da wannan mummunan ci gaba da kuma kare makomar rayuwar yara a kasashen da lamarin ya shafa.