Matsalar abinci a Sudan | Labarai | DW | 29.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar abinci a Sudan

Hukumar taimakon abinci ta Majalisar ɗinkin duniya ta yi shelar neman tallafin kuɗi dala miliyan 350 domin ciyar da yan gudun hijirar Sudan. Hukumar ta ce abincin da ake da shi zai ƙare nan da watan Janairu. Kakakin hukumar Simon Pluess, ya baiyana cewa matsalar ƙarancin abinci a Sudan ya taázzara musamman bisa laákari da taɓarɓarewar shaánin tsaro a arewacin Dafur inda mutane fiye da 350,000 suka shafe tsawon makwanni babu abinci. Watanni huɗu da suka wuce, wasu maákatan agaji su huɗu suka rasa rayukan su a yayin da suke gudanar da aiki a yankin na Dafur. Hukumar abincin ta Majalisar ɗinkin duniya, ta ce ana buƙatar dala miliyan 350 domin sayen kayan abinci wanda zaá adana gabanin faɗuwar damuna ta shekarar baɗi.