Matasan Niger Delta sun kara garkuwa da jami´an ketare 9. | Labarai | DW | 18.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matasan Niger Delta sun kara garkuwa da jami´an ketare 9.

A yankin Delta na tarayya Nigeria, matasa yan kabilar Ijaw da ke neman yancin wannan yanki,sun kara yin garkuwa, da wasu jami´an kasashen ketare da ke aikin hakko man petur.

Tun da assbahin yau ne, wani jami´in kampanin Shell, ya bayyana cewar, matasan sunyi awan gaba, da mutane 9 a cibiyar hakko mai, ta Forcados, da ke tazara kilomita 50, da birnin Warri.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya sun kame jami´ai 4, da su ka tsare har tsawan kwanaki 19.

Mutanen 19 da yan kabilar Ijaw su ka kama a yau sun hada da Amurikawa 3, da mutum 1, na Britaniyya, da 2 yan kasar Masar, 2 yan kasar Thailand ,sai kuma 1, na Phillipines.

Ranar juma´a ce da ta wuce, a shabiyun dare ,wa´adin da kungiyar, ta matasan Ijaw ta ba campanoni hako man petur na su fita daga yankin , idan kuma ba haka, ba za su ci gaba da kai hare hare yak are.

A cikin jawabin da kungiyar ta hiddo, ta sanar cewa ta shiga yaki gadan gadan ,da gwamnatin taraya, da kuma campanonin hakko man petur da ke yankin Niger Delta.