1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Musulmima Australia sun yi kira da a horasda limamai

Hauwa Abubakar AjejeAugust 22, 2005

Kungiyar musulmi matasa a kasar Australia ta ce ya kamata a sabunta tsarin koyarda addinin musulunci tare kuma da bukatar karin ilmi ga limaman kasar

https://p.dw.com/p/BvaL
Prime Minista John Howard na Australia
Prime Minista John Howard na AustraliaHoto: AP

Biyowa bayan hare haren da aka kai a Burtaniya,musulmi matasa a kasar Australia sun ce dole ne malaman addinin islama su sabunta hanyoyin da suke bi na koyar da addinin musulunci,suna masu gargadin cewa matasan musulmi da ake warewa cikin alumma suna cikin wani hadari na fadawa hannun masu mummunar akida.

Shugaban wata kungiyar musulmi matasa na Australia,Kuranda Seyit ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa, ba wai suna cewa akwai barazanar kai harin taaddanci bane a tsakanin musulmin Australia,amma akwai matasa akasar da suke goyon bayan Osama bin Ladenwanda a cewar Seyit tsohon malamin makaranta hakan zai iya tunzura tashe tashen hankula.

Seyit yace akwai bukatar sanya kananan masallatai a Australia cikin harkokin manyan masallatai na kasar,saboda a cewarsa kananan masallatan suna ci gaba da bin tsohon tsari na koyarda addinin islama,yace abin bukata anan shine a shuga tattaunawa da limaman irin wadannan masallatai.

Shugaban matasan yace rashin fahimtar musulunci tare da bada fassara maras maana ga ayoyin,ya sanya wasu masu tsatsauran raayi suke bata sunan islama.

A farkon wannan wata ne komishinan yan sanda Mick Keelty yace akwai wasu da ake zaton masu tsatsauran raayi ne su sittin a biranen Sidney da Melbourne na kasar Australia wadanda yanzu haka ake sa ido a kansu.

Kasar ta Austarlia tun bayan tura sojojinta kasashen Iraqi da Afghanistan ta shiga cikin shirin tsaro na yiwuwar kai mata hari ko dayake ba wata barazanar yiwuwar hakan.

Kwana daya kafin prime ministan Australia John Howard ya bude babban taron musulmi a babban birnin kasar Canberra,yayi kra ga shugabbanin musulmi da su sauke nauyi daya rataya a wuyansu cikin alummunsu domin kare abinda ya kira aiyukan baranda ko taaddanci.

Seyit yayi kira ga taron na Prime minister Howard daya duba shawarar da kungiyar matasan ta bayar na horas da limamai tare da yi musu rajista kafin nada su.

Yace limaman da suka taho daga yankin gabas ta rsakiya sun fito daga alummu iri daban zuwa kasar Austaralia inda aladarsu taban take saboda haka kungiyar ta yi kira ga limaman da su kai wani matsayi na cancanta kafin suyi limanci,hakazalika su kaance sun koyi harshen ingilishi su kuma san aladun kasar Australia,da siyasarta,su kuma kasance masu halaye na gari.

Kungiyar ta matasan musulmi ta kuma yi kira ga gwamnatin kasar Austaralia da ta taimaka kafa cibiyar koyarda addinin islama da zaa rika samun limamai da aka horasda su cikin a gida.

Shekaru dari biyu da suka shige musulmai suke a cikin kasar ta Austaralia,a halain yanzu muslmin kasar yawansu ya kai kashi daya da rabi na yawan jamaar kasar Australia su miliyan biyu.