1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Afirka na jin jiki a hanyar Turai

Yusuf Bala Nayaya
September 12, 2017

A cewar rahoton (UNICEF) da hukumar da ke lura da shige da ficen baki tsakanin kasa da kasa (IOM) kashi uku daga cikin hudu na matasan na ganin cin zarafi a kokarinsu na shiga Turai ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/2jllb
Libyen Falle für Flüchtlinge
Hoto: picture alliance/AP Photo/D. Etter

'Ya'yan baki da ke da buri na danganawa da kasashen Turai na fuskantar gallazawa kama daga duka da sanyasu aikin kwadago da ma'aikata lalata da su, wadanda kuma ke zama sha wuya cikin wadannan matasan na zama yara da suka fito daga yankin Kudu da saharar Afirka wadanda baya ga waccan gallazawa batu na kyamar launin fatarsu ke zama a gaba a cewar wani rahoto da ya fita a wannan rana ta Talata.

A cewar rahoton na hadin gwiwa tsakanin Asusun Kula da Kanan Yara na MDD (UNICEF) da hukumar da ke lura da shige da ficen baki tsakanin kasa da kasa (IOM) kashi uku daga cikin hudu na yaran na ganin cin zarafi karara da ma ci da guminsu a lokacin da suka kama hanya tare da masu fataucin jama'a a hanyarsu ta tsallaka tekun Bahar Rum.

Rahoton ya kara da cewa baya ga cewa bakin haure da 'yan gudun hijirar na ganin nau'oi na tijara, matasan da ke kasa da shekaru 25 su aka fi gallazawa.