Matasan ƙungiyar MEND ta yankin Niger Delta a tarayya Nigeria sun yi tare wani jirgin ruwa mai safara ɗanyan mai | Labarai | DW | 28.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matasan ƙungiyar MEND ta yankin Niger Delta a tarayya Nigeria sun yi tare wani jirgin ruwa mai safara ɗanyan mai

Matasan ƙungiyar Mend ta Niger Delta, a tarrayya Nigeria, sun kai hari ga wani tankin jirgin ruwa ,mai safara ɗanyan mai, a yau talata.

Tankin, sanfarin Escravos River, na kan hanyar sa, daga Warri zuwa tekun Atlantika.

Maharan, sun kama shi, gap ga birnin Okerenkoko,sansanin yan ƙabilar Ijaw.

Sun kwashi garaɓassar kuɗaɗe, da yawan su, ya tashi naira million 2, amma ba su yi garkuwa da kowa ba.