1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MATASA BA SA NUNA SHA'AWA GA HARKOKIN SIYASAR JAMUS.

YAHAYA AHMEDNovember 30, 2004

Alkaluma na nuna cewa, ko wane daya daga cikin matasa uku a nan Jamus ba ya sha'awar harkokin siyasa. Mafi yawan matasan kuma, ba sa daukar irin muhawarrar da ake yi a Majalisar dokoki ta Bundestag da muhimmanci. Marco Bülow, #aya daga cikin matasan da suka sami zamowa `yan majalisar ya rubuta wani littafi a kan wannan matsalar, inda yake kira ga matasan da su yi hobbasa su dau nauyin tsara makomarsu da kansu, ba tare da barinsa a hannun wasu tsirarun `yan siyasa ba.

https://p.dw.com/p/BveO
Zauren shawarwari na Majalisar dokoki ta Bundestag da ke birnin Berlin
Zauren shawarwari na Majalisar dokoki ta Bundestag da ke birnin BerlinHoto: AP

Marco Bülow na daya daga cikin matasa wadanda suka zamo `yan Majalisar dokoki ta Bundestag. Amma a daura da sauran takwarorinsa wadanda suka manyanta, baya dari-dari wajen yin kakkausar suka ga jam’iyyun siyasa, ko da ma tasa ce, idan sun yi kuskure. A cikin wani littafin da ya rubuta, wanda aka buga a kwanakin bayan nan, dan Majalisan, na jam’iyyar SPD, wadda ke mulki a halin yanzu, ya bai wa takwarorinsa matasa shawara ne kan yadda za su iya shiga cikin harkokin siyasar kasar nan, don a dama da su, ba su kasance `yan kallo kawai ba. Game da barakar da ake samu tsakanin zuriyar matasa a bangare daya da shugabannin siyasa da manyan mutane a daya bangaren, Marco Bülow na ganin cewa, matsin tattalin arziki na daya daga cikin muhimman dalilan da ke janyo hauhawar tsamarin. Sabili da haka ne ya ba da shawarar a kara kudin harajin da jama’a ke biya don samar wa gwamnati karin kudaden shiga, maimakon soke ayyukan jin dadin jama’a da gwamnati ke yi, don tsuke lalita. Kazalika kuma, ya nemi a bai wa kowa damar fadada iliminsa har zuwa inda ya ga dama, sa’annan a sassauta hargitsi da guje-gujen da ake yi fátá-fátá a ko yaushe, wai don nemna bunkasar tattalin arziki.

A nasa ganin dai, ba bunkasar tattalin arzikin kawai ne zai janyo fa’ida ga samun walwala ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne inganta halin rayuwa da jin dadin jama’a. Ya dai yi kira ga matasa `yan uwansa da su dinga hangen nesa, don su cim ma burin sabunta alkiblar halin rayuwa a nan kasar. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

"Da farko muna so ne mu janyo hankullan matasa su tashi daga barcin da suke yi..mu bayyana musu cewa, suna da angizo a kan al’amuran da ke wakana a nan kasar, ba wasu `yan tsiraru ne kawai za su iya yanke musu shawara kan yadda makomarrsu za ta kasance ba. A halin yanzu dai, mutane kalilan ne ke shiga cikin harkar siyasa, kuma mafi yawansu na tsufa. Sabili da haka ne muke bukatar matasa da yawa, wadanda za su iya tsoma baki cikin harkokin da suka shafe su, a hanyoyi daban-daban."

Babu shakka, idan aka dubi salon da matasa a nan Jamus ke bi a halin yanzu, za a ga cewa, ababa kamarsu sutura da na’urorin sadaswa na zamani kamar salula, sun fi musu muhimmanci da batutuwa kamar kare kewayen bil’Adama ko yadda za a rage gibin da ake samu a kasafin kudin kafofin inshwarar kiwon lafiya. Amma a ganin Marco Bülow, wannan kukskure ne. Kamata ya yi matasa su nuna sha’awa a harkokin siyasa. Sai dai abin takaici ne inji shi, ganin yadda babakeren da `yan mazan jiya suka yi wa kafofin siyasar nan kasar, ke hana matasan nuna sha’awar shiga cikin jam’iyyu. A cikin jam’iyyun dai sai mutum ya dade yana bauta kafin ya sami damar tsayawa takara a zabe. Marco Bülow ya ce, shi da kansa ya dandana hakan a jika. Tun yana mai shekaru 26 ne ya yunkuri tsayawa zabe, tamkar dan Majalisa, karkashin tutar jam’iyyarsa ta SPD. Amma a wannan lokacin, sai jam’iyyar ta gwammace ta tura wani dan takara daban mai shekaru 68 da haihuwa. Amma bai saduda ba. A shekara ta 2002 ne, ya sake tsayawa zaben, inda ya ci nasara, ya zamo kuma farkon matashi na jam’iyyar SPD ta jihar Nordrhein-Westfallen a Majalisar dokokin Bundestag. Ko ana daukan jawaban matasan da muhimmanci a Majalisak

Game da wannan tambayar, Marco Bülow ya bayyana cewa:-

"Kwarai kuwa. Su ma matasan, ana daukan jawabansu da muhimmanci a Majalisa, idan ba a ko yaushe ne suke son yin magana, wai don dai aji su ba. Idan suna gudanad da ayyukansu yadda ya kamata, to duk abin da suka fada, ana daukarsa da muhimmanci kamar dai yadda ake daukar na sauran `yan Majalisar wadanda suka girme musu."

Duk wanda ya karanata littafin Marco Bülkow a karo na farko dai, zai yi zaton dan Majalisar na kambama kansa ne, wajen samo zaren warware duk matsalolin da ake ta fama da su a nan Jamus. Amma a zahiri, ai babu wata kwantacciyyar hanya ta warware duk matsalolin da al’umma ke huskanta kai tsaye. Duk da hakan dai, littafin Bülkow na da muhimmanci kwarai ga matasa. Saboda ya rubuta shi ne da yin amfani da kalmomi masu saukin fahimta, ta yadda zai iya janyo hankullan matasan su ji dadin karanta shi. Ya dai yi imanin cewa, a hankali, matasa za su dinga nuna sha’awar shiga cikin tattaunawar da ake yi don fasalta makomarsu.