Matasa a yankin Niger Delta da Kamfanonin hakar man fetur | Siyasa | DW | 16.06.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matasa a yankin Niger Delta da Kamfanonin hakar man fetur

kokarin da ake na ceto wadanda akayi garkuwa dasu a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur

default

Ya zuwa yanzu dai tuni gwamnatin jihar Bayelsa dake kudu maso gabashin kasar ta Nigeria ta dukufa kain da nain wajen ganin an sako wadannan mutane guda shida,biyu daga cikin su Jamusawa ragowar hudun kuma yan Nigeria.

Idan dai za a iya tunawa a jiya ne matasan wadanda suka daurewa karya gindi ta hanyar tashe tashen hankula da kuma rikice rikice a yankin na Niger Delta sukayi garkuwa dasu a yayin da suke cikin jirgin ruwa a hanyar su ta zuwa Jihar ta Bayelsa daga jihar Delta duka dai a yankin na Niger Delta.

A cewar kakakin kamfamnin na B da kuma B,tuni gwamnatin ta Bayelsa ta fara tattaunawar sulhu da matasan a kokarin da take na ganin an sako mutanen guda shida ba tarte da wani daga cikin su yaji rauni ba ko kuma ya galabaita.

Ya zuwa yanzu ma dai a cewar kakakin tattaunawa game da sako mutanen tayi nisa a wani lokaci a nan gaba kadan wadan nan mutane zasu samu yancin su kamar yadda suke dashi a can baya.

Game kuwa da halin da mutanen ke ciki, kakakin kamfanin yaci gaba da cewa dukkannin mutane shidan na cikin kwanciyar hankali da lumana,domin kuwa matasan sun basu damar ganawa dasu ta hanyar wayar tarho.

A waje daya kuma a cewar wata sanarwa data fito daga bangaren matasan, ta shaidar da cewa matasan sun dauki wannan matakin ne don tursasa bangaren kamfanin na shell cika alkawarin da yayi musu na samar da aikin yi ga wasunsu a hannu daya kuma da gudanar da aikin ci gaba a yankunan dav kamfanin ke gudanar da aiyukan sa.

A daya hannun kuma kamfanin na shell ya tabbatar da cvewa a shekarta ta 2002 data gabata,kamfanin ya cimma yarjejeniya da wasu kungiyoyin al,ummar yankunan da yake hakar mai guda tara akan zai gudanar da aiyukan ci gaba a yankunan.

Bisa hakan a cewar kakakin kamfanin na shell, kamfanin nasu ya samu damar aiwatar da wasu aiyukan, to amma ragowar za a kammala su ne a cikin wannan shekara da muke ciki izuwa shekara ta 2011.

A cewar kakakin kafin yin garkuwa da wadannan mutane shidan kamfanin ya shirya gudanar da wani taro a tsakanin sa da alummar yankin na Iduwini don yi musu cikakken bayanin dalilin daya sa za a dauki lokaci mai tsawo kafin gudanar da wadan nan aiyuka da sukayi alkawarin gudanarwa a yankin.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa rikice rikice da tashe tashen hankula abubuwa ne da suka dade da zamowa ruwan dare a yankin na Niger delta, a kokarin da mutanen yankin keyi na samun ingantar rayuwar su, musanmamma a tsakanin su da kamfanoni masu hakar mai a hannu daya kuma da gwamnatin tarayya.

Bugu da kari bayanai sun shaidar da cewa sau da yawa ire iren wadan nan matasa kanyi garkuwa da jamian kamfanin mai a yankin to amma daga baya sai a sasanta a sako su ba tare da sun tagayyara ba ko kuma sun sha bakar wahala.

A dai wannan yanki na Niger Delta ne tarayyar ta Nigeria ke hako danyan man fetur din da yawan sa ya tasamma gagga miliyan biyu da digo uku a kullum Ranar Allah ta,ala.

 • Kwanan wata 16.06.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbJ
 • Kwanan wata 16.06.2005
 • Mawallafi ibrahim sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbJ