1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa a yammacin Jamus shekaru 20 bayan haɗewa

September 30, 2010

Kimanin kashi 20 cikin ɗari na Jamusawa ba su shaidar da rarrabuwar ƙasar ba saboda an haife su ne bayan 1990. To ko shin mene ne ra'ayinsu game da haɗewar Jamus? Kuma yaya alaƙarsu take da juna?

https://p.dw.com/p/PPzj
Ɗalibai a ajin tarihi a sakandaren St. IrmgardisHoto: DW

Galibi dai Matteo Brossette ya kan tashi daga barci ne a makare. Ba da wata-wata ba ya kan yi wanka ya sanya tufafinsa ya sha gahawa sannan ya kama hanyarsa ta zuwa makaranta. Ya kan isa ƙofar makarantar a daidai lokacin da ake kaɗa ƙararrawa ta shiga ajujuwa. "Abin farin ciki shi ne kasancewar babu wata tazara ta a zo a gani tsakanin gidamu da makarantar. A saboda haka tsakanina da makaranta kamar dai tsakanin ofishin malamai ne da ɗakunan aji."

Matteo na halartar makarantar sakandare ne ta St. Irmgardis a yankin Bayenthal dake kudancin birnin Kolon. Galibi masu matsakaicin ƙarfi su ne suka fi sha'awar zama a wannan yanki.

Ga ɗalibai dai wani lamari ne na tarihi

Petra Linßen malamar tarihi ce kuma darasinta a yau ya jiɓanci tarihin Jamus ne na baya-bayan nan. Ta tambayi ɗalibanta ko cikinsu akwai wanda ya taɓa kai ziyara a katangar Berlin. Kusan ma rabin ɗaliban ko kashi biyu bisa uku daga cikinsu sun kai ziyara yankin. "A ɓangaren yammaci dai an yi wa katangar zane iri-iri to ko kun san yadda ɓangaren gabaci ya kasance?" Wani ɗalibi ya ba da amsa cewar: "Ba kome a wurin."Na'am haka ne ba wanda ke da ikon yi wa katangar zane a wancan ɓangaren - amma me ya sa hakan, in ji malamar. "Dalili shi ne ba wanda ke kurarin kusantar katangar", in ji wata ɗaliba. Lalle haka ne saboda wayoyi masu kisa da aka karkafa da kuma hasumiyar gadi da aka gina.

Jamus ta Gabas, rushewar katanga, sake haɗewar Jamus - dukkan waɗannan abubuwan matasa masu shekaru 17 ko 18 da haifuwa su kan naƙalce su ne a finafinai. Duka-duka abin da suka sani shi ne haɗaɗɗiyar ƙasar Jamus: "Ba na zaton cewar akwai wata katanga a tunanin mutane, saboda ni kai na na taso ne a haɗaɗɗiyar ƙasar Jamus." Sauran ɗaliban sun girgiza kawunansu don nuna amincewarsu.

Kusan babu sauran banbanci

Thomas Gensicke masanin kimiyyar zamantakewa ne a cibiyar binciken al'amuran zamantakewa ta TNS dake birnin Munich. A cikin bayanin da yayi yayi nuni da cewar shekaru 20 bayan haɗewa a yanzu an wayi gari dukkan matasa na gabaci da yammaci sun zama gungu ɗaya ta yadda ba wani banbanci tsakaninsu. Amma idan an lura da idanun basira za a ga cewar ta fuskar kuɗi matasa a yammaci sun fi morewa. A sakamakon haka matasan na gabaci ba su da ƙwarin guiwa game da makomarsu, suna tattare da fargaba a game da makomar rayuwarsu bisa saɓanin takwarorinsu a yammaci. Sai dai kuma a ganin Thomas Gensicke hakan ba wani abin mamaki ba ne: "Domin kuwa muna da ninkin marasa aikin yi tsakanin matasa a gabaci."

Matteo dai ba ya da wata matsala ta rayuwa saboda iyayensa na da wadata iya gwargwado. Fatansa shi ne ya kammala sakandare da gagarumar nasara ya koyi fasahar zane a jami'a kana daga baya ya ci gaba da rayuwarsa a wata ƙasa ta ƙetare - in kuwa so samu ne da zai fi ƙaunar zama a Madrid ta Spain.

Kiɗa ne ya fi ɗaukar hankali

Bayan faɗuwar rana Josephine ta iso daga wani yanki dake wajen Kolon. Josephine dai ƙawa ce ga Matteo kuma dukkansu biyu sai suka zarce zuwa cikin gareji, wanda Matteo ya mayar da shi tamkar ɗakin kiɗa. Matteo kan buga fayafayayi a klob-klob ɗin Kolon kuma shi kansa ya kan sarrafa nasa kiɗan. Ya fara nuna wa Josephine wasu daga cikin kiɗe-kiɗen nasa.

Shi dai Matteo ba abin da ya sha masa kai a rayuwa face kiɗa. Kuma ko da yake yana sha'awar al'amuran siyasa, amma ba ya kutsa kansa a ciki. A sakamakon haka, a lokacin wani biki na kiɗa a garin Leipzig, nan da nan ya lura cewar matasa a gabacin Jamus na sha'awar al'amuran siyasa matuƙa ainun. Ya ce ya lura da zane iri daban-daban a ƙananan rigunan da matasan ke sanye da su kama daga maganar adawa da masu tsattsaran ra'ayin ƙyamar baƙi zuwa ga kiran zaman lafiya a maimakon yaƙi. A nan yammaci galibi akan ga irin waɗannan abubuwan ne lokacin zanga-zanga. Amma a gabaci za ka gansu sanye da ire-iren waɗannan ƙananan riguna masu ɗauke da batutuwan siyasa a ko'ina, in ji Matteo. Bisa ga dukkan alamu mutane a gabacin Jamus ba su wata rufa-rufa game da ra'ayinsu na siyasa.

Ita ma Josephine ta taɓa naƙaltar irin wannan lamari ko da yake ta wata manufa dabam. Ta kaɗu game da wasu matasa da ta gani a wani ɗan ƙaramin ƙauye dake kusa da Usedom a jihar Mecklenburg-Vorpommern a gabacin Jamus. Ta ce: "Lokacin da na kai ziyara Usedom na je wani ɗan ƙaramin ƙauye, inda kusan dukkan mazauna ƙauyen na sauraron kiɗan ƙungiyar Böhze Onkelz." Wannan ƙungiyar, ko da yake tana musunta kasancewa 'yar tsattsauran ra'ayin wariya, amma kuma ta shahara tsakanin masu wannan aƙida. Josephine ta ce: "Wannan abu ya tsoratar da ni. A nan ma matasan na yawo ne a cikin ƙananan riguna dake ɗauke da zanen ƙungiyoyi masu aƙidar wariya."

Matasa a yammaci sun fi kusa da "Tsarin Mulkin Tarayya"

Hatta a gabacin Jamus masu aƙidar wariyar 'yan tsiraru ne in ji malamin binciken al'amuran masata Gensicke. Sai dai abin da ya lura da shi shi ne a gabacin Jamus matasan kan saka ayar tambaya a game da al'amuran siyasa da tattalin arziƙi da zamantakewa a Janhuriyar Tarayyar Jamus bisa saɓanin takwarorinsu a yammaci. Musabbabin haka shi ne kasancewar a yammacin Jamus iyayen yara da makarantu da kafofin yaɗa labarai na yayata tsarin tarayyar fiye da gabaci.

Sai dai kuma Josephine na ganin cewar zata iya komawa da zamanta a gabacin Jamus, amma fa a birni. Matasa 'yan ƙalilan ne a yammaci ke da kyakkyawan zato game da gabaci kamar Josephine.

Ga ra'ayin da dama daga cikinsu a yammaci ne mutum ke da kyakkyawar kafa ta samun ilimi da aikin yi don kyautata makomar rayuwarsa. Amma fa hatta a gabacin ma matasa na yankin sun fi ƙaunar zuwa yammaci don kyautata makomar rayxuwarsu saboda a ganinsu a yankin ne tsarin mulkin tarayya ke tafiya salin alin ba tare da wata tangarɗa ba.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal