Matan shugabannin kasashen Afirka: Mulki a bayan fage
Ba wai an zabe su bane, sai dai suna da karfin fada a ji sosai a gwamnati. Wasu matan shugabannin kasashen Afirkan ma na fatan zama shugabannin kasa. Ga matan da ke bayan shugabannin Afirka.
Grace Mugabe: A baya abar dariya, yanzu kuwa abar tsoro
Tsawon lokaci tana tare da Shugaba Robert Mugabe inda suke da 'ya'ya biyu, koda yake yana tare da matarsa ta farko. Grace ta zama matar shugaban kasa bayan da matar Mugabe ta mutu. A yanzu haka ita ce shugabar mata ta jam'iyya mai mulki a Zimbabuwe ZANU-PF, inda take da fada a ji sosai. Duk da tana musantawa, da dama na ganin ita ce za ta gaji mijinta da ke da shekaru 92 a duniya a yanzu.
Aisha Buhari: 'Matar shugaban kasa'
'Yan Najeriya da dama sun yi mamaki lokacin da Aisha Buhari ta sanar da cewa za ta girmama kundin tsarin mulkin kasar, ba za ta shiga cikin siyasa ba. Sai dai za ta rinka gudanar da ayyukan jin kai. A yayin da ya karbi mulki, mai gidanta Shugaba Muhammadu Buhari, ya rusa ofishin matar shugaban kasa yana mai cewa barna ce da kudin al'umma, kana ya saba wa kundin tsarin mulki.
Margaret Kenyatta: Abar soyuwa ga 'yan kasa
Al'ummar kasar Kenya na son matar shugabansu. Margaret Gakuo Kenyatta ta janyo hankalin al'umma ne ta hanyar gangaminta na rage mace-macen mata masu juna biyu yayin haihuwa da kuma kananan yara. Babanta dan kasar Kenya ne ma'aikacin hukumar kula da layin dogo, mahaifiyarta Bajamushiya, ana yi wa Uwargida Kenyatta kallon mai nutsuwa da tsan-tseni. Ta auri Shugaba Uhuru Kenyatta a shekarar 1991.
Ana Paula dos Santos: Daga ma'aikaciyar jirgin sama zuwa matar shugaba
Ana Paula dos Santos ta yi aiki a matsayin mai kula da fasinjoji a jirgin sama kana kuma mai tallan kayan ado. Ta hadu da mijinta shugaban kasar Angola Jose Eduardo dos Santos, yayin da take aiki a jirgin saman sojoji na Angolan kirar Air Force One. Yayin da wasu ke yaba mata kan kokarinta na kyautata rayuwar mata da kananan yara, wasu na sukanta da yin rayuwa mai tsada.
Dominique Ouattara: Hadari ga maza?
Dominique Ouattara ko yaushe tana son yin mu'amala da manyan mutane. Yayin da ta hadu da shugaban kasar Ivory Coast Allasane Ouattara a karshen shekarun 1980, ta kasance 'yar kasuwar da aka sani a duniya. Bayan da ta auri Ouattara ta sake bunkasa harkokin siyasarta a kasar. Ta kuma mayar da hankali kan gidauniyarta ta kare 'yancin yara.
Janet Museveni: Matar shugaban kasa ta din-din-din a Yuganda
Janet Museveni ta kwashe shekaru 30 a matsayin matar shugaban kasa a Yuganda, wadda kuma ta fi dadewa a nahiyar Afirka. Bayan nasara a zaben shugaban kasa mai cike da rudani da mijinta Yoweri Museveni ya samu, za ta ci gaba da rike mukaminta zuwa wani lokaci. Uwa ga yara hudu, tun a shekarar 2006 ta zamo 'yar majalisa, kuma a watan Yunin da ya gabata mijinta ya bata ministar wasanni da ilimi.
Marieme Faye Sall: Matar kulle ga shugaban kasar Senegal
Matar shugaban kasar Senegal 'yar kasa ta farko Marieme Faye Sall daga dama tare da matar shugaban kasar Amirka Michelle Obama a hagu, ita ce matar shugaban kasa 'yar asalin kasar ta Senegal, duk sauran asalinsu Faransawa ne. An bayyana ta a matsayin matar kulle wadda da wuya ta shiga cikin harkokin mulkin Shugaba Macky Sall. Sai dai suna shan suka dangane da dabi'arsu ta 'yan ra'ayin mazan jiya.
Marie Olive Lembe: Mai taka tsan-tsan da taimako
Tsawon shekaru aka yi mata baiko da Shugaba Joseph Kabila na Kwango. A shekara ta 2006 ta zamo matar shugaban kasa. Marie Olive Lembe di Sita na da 'ya'ya biyu da mijinta. An tabbatar da cewa tana da dangantaka ta kut da kut da Jaynet Kabila, 'yan biyun Shugaba Kabila, wacce ke matsayin ta hannun damansa. Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango na da matayen shugaban kasa biyu.
Afirka ta Kudu: Ko matar shugaban kasa ta ainihi za ta tashi tsaye?
A shekara ta 2008 aka yi bikin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma. Cikin shekaru hudu ya auri mata uku: Nompumelelo Zuma da Thobeka Zuma da Bongi Ngema-Zuma. Yana da matarsa ta farko Sizakelle da suka shafe shekaru. Tsohuwar matarsa shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Afirka, Nkosazana Dlamini-Zuma na amfani da sunansa. Ana sukar wannan aure-aure na Zuma da taimaka wa masu kin biyan haraji.