Matan karkara a Nijar: Ana ci da guminmu | Zamantakewa | DW | 25.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matan karkara a Nijar: Ana ci da guminmu

Matan karkara a Jamhuriyar Nijar sun koka da yadda matan birane ke rawa da bazarsu, a dai-dai lokacin da kungiyoyin mata ke zanga-zangar neman hakkinsu a gwamnati.

Ayarin mata dauke da karan hatsi da suka kwaso a gonakai, a wani kauyen garin Maijirgi cikin karamar hukamar Tasawa a jihar Maradi ne suka yi wannan koke. Wata mata cikinsu ta ce wahalar da suke sha bayan debo ruwa a rijiya su na debo kara a gonakai, kana su shiga girki baya ga kulawa da yara. 

Da wakilinmu Mahaman Kanta ya kara gaba a wani gari da ake kira Gazuwa, nan ko ya ziyarci masussuka inda ya tarar da matan suna kwadagon sussuka wadanda yawancinsu dattijai ne. Suna sussuka o wane dami daya akan ladan kudi CFA 200. Wata Gyatuma mai suna Iya Hauwa ta ce da ya ke ta tsufa a wuni bata wuce sussuke dami uku ba, amma masu karfi suna sussuke har dami biyar.

Da aka tuntube su kan kokowar da shugabanninsu na Yamai suke yi na neman hakkinsu,  matan sun ce basa ganin komai. Sai rana-rana suka kewayo su kira taro, su je su tarbesu suna ta tabi cikin rana, amma daga wannan basa ganin komai. Saboda haka matan karkarar suka yi kira ga shugabannin nasu na bariki da cewar idan sun kaso su dinga tunawa da su na ganin irin halin kuncin talaucin da suke ciki.