Tambaya daga Ibrahim Ibbo dake Kancari a ƙasar Burkina
Faso, ya na so ne a gaya masa matan da suke riƙe da
muƙamin shugaban ƙasa ko shugaban gwamnati duniya a
halin yanzu.
A yankin Latine Amurika, ƙasar Arjentina Isabel Peron ta
kasance mata ta farko a wannan yankin da ta taɓa hawa
karagar mulkin shugabacin ƙasa daga shekara ta 1974 zuwa
1976.Sai kuma Cristina Kirchner da aka zaɓa a shekara ta
2007 wadda yanzu haka ke riƙe da ragamar jagorancin ƙasar
Arjentina.
A ƙasar Chili akwai Michel Bachelet da aka zaɓa shugabar
ƙasa a watan Janairu na shekara ta 2006,to saidai a halin
yanzu ta zo ƙarshen wa´din mulkinta
A ƙasar Philipines kuwa, Glorio Aroyo mataimakiyar shugaban
ƙasa Joseph Estrada da aka hamɓarar da shi dalili da
al´amuran cin hanci da karɓar rashawa ta maye gurbinsa a
watan Janairi na shekara ta 2001, sannan a ka zaɓe ta a
matsayin shugabar ƙasa mai cikkaken mulki a shekara ta
2004.
Idan muka koma Indiya kuwa, Pratibha Patil ce ta taɓa zama
mace shugaban ƙasa bayan ta lashe zaɓe a watan Juli na
shekara ta 2007.
A nan nahiyar Turai an zaɓi Tarja Halonen a matsayin
shugabar ƙasar Finlande a shekara ta 2000, sannan aka sake
zaɓen ta karo na biyu a watan Janairun shekara ta 2006.
A Irlande,an zaɓi Mary Robinson a matsayin mace ta farko a
kujerar shugaban ƙasa, kuma mace yar uwarta, wata
takwararta mai suna Mary McAleese ta gaje ta an zaɓe ta a
shekara 1997, aka kuma sake zaɓenta karo na biyu a shekara
ta 2004.
Sai a Lituaniya a ranar 18 ga watan Mayu na shekara ta 2009
aka zaɓi Dalia Grybauskaite.
A ƙasar Swizland shugabar Doris Leuthard majalisar
Tarayya ta dorawa yaunin jagoranxcinkasar daga shekara ta
2010, saidai cemma kamin ita akwai mata biyu da suka taɓa
jagorancin wannan ƙasa.
A nahiyarmu ta Afrika kuwa, shugabar ƙasar Liberia ce Elen
Searlef Johnson ta taɓa hawa wannan kujera mai alforma.
An zaɓe ta a watan Nowemba na shekara ta 2005.
Idan muka koma ɓangaren shugabanin gwamnati kuwa,a nan
ƙasar Jamus Angela Merkel ta zama shugabar gwamnati ta
farko tun daga watan Nowemba na shekara ta 2005.
Sannan a ƙasar Island,Johanna Sigurdardottir ce ta taɓa
hawan kujera shugabar gwamnati a shekara ta 2009.
A Krotiya Jadranka Kosor ita ce mace ta farko da ta hau
muƙamin Firaminista shugabar gwamnati.Saki kuma akasar
Ukraine inda Iouliya Timoshenko ta hau wannan matsayi a
shekarar 2005 da kuma 2007.
A Bangladesh Cheick Hasina Wajed, tayi zama shugabar
gwamnati daga 1996 zuwa 2001.Sannan ta sake hawa a
watan Janairun shekara ta 2009.
To saidai fa a halin da ake ciki yanzu duniya ta cenza, mata
na cigaba da ƙara kutasawa ana damawa da su cikin
harakokin siyasa.Idan ba a manta ba a ƙarshen shekara ta
2008, Hilary Clinton Sakatariyar harakokin wajen Amurika mai
ci yanzu tayi hoɓasarmar tsayawa takarra shugabancin ƙasar
Amurika.Haka zalika a ƙasar Faransa a zaɓen shugaban ƙasar
da ya wakana shekaru ukku da suka gabata,saura ƙiris
Segoléne Royal ta jam´iyar PS ta lashe zaɓen.
Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala