1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Turai.

June 4, 2010

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sa ƙaimi a yaƙinta da miyagun ƙwayoyi.

https://p.dw.com/p/Nhhe
Jose Manuel Barroso , shugaban hukumar zartarwa ta Ƙungiyar Tarayar Turai(EU).Hoto: AP

A taron da suke yi a ƙasar Luxembourg, ministocin cikin gida na ƙasashen Tarayyar Turai sun daidata kan ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da safarar miyagun ƙwayoyi. Ministocin sun ce wannan mataki zai haɗa ne da toshe hanyoyin da ake amfani da su wajen shigowa da ƙwayoyin heroin da cocaine, ƙasahen Turai. An ɗora wa ƙasar Jamus alhakin sa ido akan hanyoyin da ake bi da ƙwayoyi daga ƙasashen yankin Balkan da kuma Afganistan. Ita kuwa Faransa aikinta shine ƙwace jiragen ruwa masu jigilar cocaine zuwa Turai daga iyakokin kudancin Turai musamman daga yammacin Afirka. Ministocin sun kuma tsai da shawarar ƙwace kadarori a matsyin ɗaya daga cikin matakan da za su ɗauka. Ƙiyasi ya yi nuni da cewa kuɗin cocaine da ake cinikinsa a Turai a kowace shekara ya kai euro miliyan dubu tara.

Mawallafiya:Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu