1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

070610 Sparpaket Entwicklungshilfe

June 8, 2010

A wani mataki na riga kafi, gwamnatin Jamus ta ɗauki matakan tsuke bakin aljihu, to amma bai shafi taimakon raya ƙasa ba.

https://p.dw.com/p/NlZJ
Jamus ta tsuke bakin aljihuntaHoto: picture alliance/dpa

Gwamnatin ƙasar Jamus ta sanar da wani tsarin tsuke bakin aljihu, domin riga kafi ga  koma bayan tattalin arziki da wasu ƙasashen Turai suka sami kansu ciki. Sai dai wannan matakin ba shafi,taimakon raya ƙasa ba, da Jamus ke baiwa ƙasashe masu tasowa.

 Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kanta ta fito fili ta bayyana cewa, Jamus tana kan bakanta na cika ƙa'idar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙayyade, wato na cewa ko wace ƙasa ta ware ɗigo bakwai cikin ɗari na kuɗin shiga da ta ke samu, domin baiwa ƙasashe masu tasowa agaji, Merkel ta ce:Zamu cika alƙawarin, kuma ina iya tabatar muku cewa bamu dakatar da kasafin bada agaji da muke yi ba. Amma bamu yi wani ƙari ba akai, kamar yadda wasu ministoci suka nema. Wannan manufar abune da ba mai sauƙi ba.

Ministan raya ƙasashe Dirk Niebel ya buƙaci a samar da ƙarin taimakon da Jamus za ta riga bayawar, inda yanzu yace Jamus za ta yi ƙarin Euro miliyan ɗari huɗu. Misali ta fannin ilimi da fannin bincike, zai samu ƙarin kuɗi a shekara mai zuwa fiye da bana.

Wannan dai yana nufin ministan kula da raya ƙasashe da kuma ministan kuɗi Wolfgan Shäuble, za su gana bada jimawa ba, domin duba wannan lamari. Shi kuwa sakataren raya ƙasashe  na Jamus Hans-Jügen Beefeltz, yace duk da irin wannan halin da ake ciki, batun bada taimakon raya ƙasashe abune dake samun goyon bayan jama'a:

Kusan ko wane lokaci, biyu bisa ukku na Jamusawa, suna cewa, duk da irin lokacin da ake fiskantar matsalar tattalin arziki, kamata ya yi gwamnatin Tarayyar Jamus ta sauke nauyin dake kanta na bada agajin ƙasa da ƙasa, musamman a ƙasashen duniya dake fama da 'yunwa.

Sakataren ya ƙara da cewa a shekara mai zuwa za su bada taimakon kimanin Euro miliyan 600, domin a cika alƙawarin dukkan taimakon raya ƙasashe. Daga cikin taimakon akwai batun kare mahalli . Jami'in ya kuma bayyana cewa, a wannan sherar ma Jamus ba za ta iya cika  ƙa'idar da ake so ba. Ƙasar Jamus dai tana ware kasafin kuɗi don bada agaji wanda ya haura Euro miliyan dubu shidda.

Mawwallafi: Usman Shehu Usman Edita: Umaru Aliyu