1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin korar 'yan Afirka daga Isra'ila

January 29, 2018

Hukumomin Isra'ila sun bukaci ficewar bakin haure 'yan kasashen Afirka, saboda abin da ta bayyana na zamansu matsala ga kasar. A makonnin da suka gabata ne gwamnatin ta Isra'ila ta sanar da hakan tare da tayin bai wa bakin na haure wasu kudade.

https://p.dw.com/p/2rhXz

Mahukuntan kasar Isra'ila sun tsaya kan matakin korar Afirkawan da ke zama a kasar. Faraministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ya shaidar da hakan ya bayyana bakin hauren a matsayin  'yan kutse' ga Isra'ilar’ Firaministan ya shaida haka ne lokacin wani zaman da majalisar zartaswar kasar ta yi. 

A nasu bangaren, bakin hauren, suna zargin Isra'ila tana son tura su zuwa kasashen Yuganda da Ruwanda.

Kasar dai ta yi tayin bai wa 'yan hijran dala $3,500 da kuma daukar nauyin tikitin komar da su kasashen da suka fito.