1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin koran baƙin haure a Faransa

Halimatu AbbasJuly 29, 2010

Faransa ta kama hanyar fatattakar baƙin haure da suka haɗa da 'yan Gypsy

https://p.dw.com/p/OXZY
Wasu mata da yara 'yan GypsyHoto: AP

Shugaba Nikolas Sarkozy na Faransa, ya ba da umarnin koran 'yan ƙabilar Gypsy da suka shiga ƙasarsa ba akan ƙa'ida ba. Ya kuma yi kira da a wargaza sansanoninsu. Hakan ya samu ne sakamakon tattaunawar gaggawa da Sarkozy ya buƙaci a gudanar a matsayin ɓangare na yaƙin da ya ayyanar akan miyagun lefuka da kuma masu ta da zaune tsaye, a biranen ƙasar. Jami'an gwamnati sun yi wannan zaman ne, bayan da aka yi arangama tsakanin 'yan Gypsy da 'yan sanda a farkon wannan wata bayan da 'yan sandan suka bindige wani matashi da ke guje wa shiga hannunsa a garin Loire Valley.

Sarkozy ya ce za a hukunta duk wanda ke da hannu a cikin wannan ɗauki-ba-daɗin. Ministan cikin gidan Faransa, ya ce akwai sansanonin kimanin 300, da aka kakkafa ba a kan ƙa'ida ba, da ke zaman matsugunai ga 'yan Gypsy da kuma matafiya. Ya ce za a rufe waɗannan sansanoni nan da watanni uku, kuma 'yan Gypsy waɗanda ba 'yan asalin wannan ƙasa ba ne, da ke aikata miyagun lefuka za a koma da su ƙasashensu na asali.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu