1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin karshe na zaben yan majalisun dokoki a kadar Masar

December 1, 2005
https://p.dw.com/p/BvIe

Yau ne a kasar Masar a ka shiga zagaye na 3, kuma na karshe a zaben yan majalisun dokoki.

A baki daya zaben na yau ya shafi kujeru 136, na yan majalisa a jihohi 9 na kasa.

Za a yi zagaye farko yau alhamis, sannan zagaye na 2 ranar 7 ga watan da mu ke ciki.

Kungiyar yan uwa musulmi ta jera yan takara 49 a wannan zabe.

A matakai 2, da su ka gabata, kungiyar ta zargi jami´an tsaro da wasu karnukan farautar gwamnati, da hadasa hargitsi da magudi , saidai duk da haka, kungiyar yan uwa musulmi ta sami kujeru 76, abinda ta dauka wata gagaramar nasara.

Kasar Amurika, ta yi kira ga shugaba Osni Mubarak na Masar da ya dauki mattakan da su ka dace, domin shirya adalci a zaben.