Matakin da Saudiyya ta dauka akan maniyyata | Labarai | DW | 25.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakin da Saudiyya ta dauka akan maniyyata

Haj/Saudi

Kasar Saudi Arabia tace yazuwa yanzu fiye da maniyyata aikin Hajjin bana rabin miliyanne suka isa kasar kuma dukkanninsu an an bincikesu domin tabbatar da cewa kalau suke basa dauke da wasu cututtuka,saboda fargabar da ake ta bazuwar cutar murar tsuntsaye a duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito ministan kula da lafiya na Saudiyan Hamad al Manei yana cewa maniyyatan su dubu dari shida da ashirin da biyu da suka hallara kawo yanzu don fara aikin hajjin wanda za a fara a cikin sati na biyu na watan janairu na sabuwar shekara dukkaninsu an kammala bincikensu.

Ministan ya ce a wannan karan sun tsaurara matakan binciken lafiyar maniyyata a dukkanin kafofin .shigowa kasar kuma duk maniyyacin da aka samu yana dauke da wata cuta suna maida shi kasarsa nan take.

Sai dai bai bayyana yawan maniyyatan da aka maida kasashen nasu ba a sakamakon wannan mataki da suka daukan.