MATAKIN DA SAUDIYA TA DAUKA NA YAKI DA YAN TAADDA. | Siyasa | DW | 19.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MATAKIN DA SAUDIYA TA DAUKA NA YAKI DA YAN TAADDA.

Bayan wasu munanan hare haren kunar bakin wake da suka gudana a kasar Saudi Arabia,a yanzu haka mahukuntan kasar sun gabatar da kamfe din kawo karshen masu tsattsauran raayin kasar da suke da alaka da kungiyyar Alqaeeda,ta Usama bin Laden wacce ake zargin cewa ta yan kunar bakin wake ce.

Ba,a da bayan wannan dalilin,gargadi da mahukuntan Amurka suka bayar ga yan kasar su dake da zama a kasa mai tsarkin na ranar 17 ga watan disanbar nan da muke ciki na cewa akwai alamun babu dadewa yan kunar bakin wake zasu kara kai wani sabon hari wannan dalilin na daya daga cikin dalilan daya haifar gwamnatin ta Saudiya ta dauki wannan mataki na yaki da tsagerun yan taaddar da kuma masu tsattsauran raayin kasar dake da alaka da kungiyyar ta Al,Qaeeda.

Bayanai dai sun nunar da cewa a tun lokacin da mahukuntan Amurka suka gano cewa mutane 15 daga cikin 19 da suke zargi sun kai harin nan na Sha daya ga watan satumba yan kasar Saudiya ne dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta fara tsami,bayan kuwa a baya kasar ta Saudiya na daya daga cikin babbar kawa ga kasar ta Amurka a kasashe dake yankin Gulf ko kuma ma ace duniya baki daya.

Haka kuma a bayan harin ne,mahukuntan na Amurka suka shiga takun saka da kuma zargi ga mahukuntan na Saudiya cewa tsarin addinin islamar su shine yake kyankyasar masu tsattsauran raayin kasar,wadanda ake hada baki dasu wajen aikata irin wadan nan munanan aiyukan na hare haren kunar bakin waken.

Bugu da kari a baya lokacin dangantaka a tsakanin kasashen biyun na tafiya dai dai wa dai da, Amurkan ta jibge sojojin ta ne a birnin Riyad na kasar ta Saudiya,amma lokacin da akayita ware a tsakanin kasaashen sai kasar ta Amurka ta mayar da sojojin nata izuwa kasar Kuwait da kuma Qatar dake yanki daya da kasar ta Saudi arabiya.

A dangane da haka ne a yanzu haka mahukuntan na saudiya sun dauki gabarar saka wando daya da duk wani mai tsattsauran raayi a kasar dake da alaka da kungiyyar Alqaeeda tare da tabbatar da kyakkyawan tsaro a fadin kasar baki daya dangane da barazanar da ake kai kawon ta na kawo wani sabon hari na kunar bakin waken a cikin kasar.

A cewar yarima mai jiran gado na Saudiya Abdullah Bin Abdulaziz,wannan mataki da kasar ta Saudiya ta dauka na yaki da tsagerun yan taaddar kasar shiri da kuma zai wayarwa da sauran mutanen kasar da kuma ma na duniya cewa addinin islama addinine wanda yayi hannun riga da taaddanci,kann yadda wasu suka dauka cewa mazaunin su daya.

A yanzu haka dai rahotanni daga kasar ta Saudiya sun nunar da cewa,taho mu gama da jamian tsaron kasar ta Saudiya keyi tsakanin su da tsagerun kasar masu aikata aikin taaddanci abune daya zamo ruwan dare a cikin kasar,sakamakon irin matakin da mahukuntan kasar suka dauka na kawo karshen su a cikin kasar baki daya.

Bugu da kari rahotannin sun kuma nunar da cewa duk wata kafa ko kuma kungiyya da ake zargi na turawa masu tsattsauran raayin taimako na kudi an saka mata ido,don kawo karshen ta tare da tuhumarta da aikata aikin ashsha.

A dai watan Oktoba daya gabata na wannan shekarar da muke ciki mahukuntan kasar suka bayar da sanarwar gudanar da zabe na yan majalisar karamar hukumar birni da kewaye,wanda da dama daga cikin masu nazari na kasar ke kallon sa a matsayin mataki na dawowa turbar dimokradiyya.