Matakin Baharain kan wani malamin Shi′a | Labarai | DW | 21.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakin Baharain kan wani malamin Shi'a

Gwamnatin Baharain ta soke takardar izinin zama dan kasa ga wani babban shehin malamin Shi'a na kasar wanda ya yi fice wajen sukar lamirin mahukuntan kasar mabiya tafarkin Sunna.

Ministan cikin gidan kasar ta Bahrein ya ce suna zargin Sheikh malamin Issa Qassem da kasancewa dan barandan wasu kasashe na ketare da kuma neman yada rikicin addini a cikin wannan kasa ta yankin Golf wacce tun a shekara ta 2011 take fama da tarzoma lokaci zuwa lokaci.

Saidai kuma a cikin wata sanarwa da Qassem Soleimani daya daga cikin shugabannin sojin kasar Iran ya fitar a kamfanin dillancin labarai na Tasmin a matsayin martani, ya ce wannan mataki da hukumomin Bahrein suka dauka kan wannan malamin Shi'a na shirin rura wata wutar tarzoma a yankin na Golf domin kuwa mataki ne da Iran ba za ta taba amincewa da shi ba