Mataki maimakon kalamai: Fafutukar mata
Sun sha duka da barazana gami da dauri: Amma masu fafutuka saboda 'yancin mata na kada kuri'a ba su saduda ba. A Birtaniya burin ya cika a farkon watan Febrairu na shekarar 1918. Kafin lokacin daguwar hanya ce.
Amfani da karfi fiye da kima
Maza suka mamaye harkokin mulki kuma suna son ci gaba da rike komai. Saboda haka a farkon karni na 20, 'yan sanda sun yi amfani da karfi kan mata masu mafutuka. Bayan sun nemi shiga harkokin siyasa. Wannan bai samu ba sai a shekarar 1918.
Wayo da hanzari
Emmeline Pankhurst ta kasance wadda ake gani a matsayin wadda ta kafa kungiyar gwagwarmaya kan 'yancin mata. Da jawabai masu kwarjini ta yi kokarin samar da 'yancin zabe ga mata. Lokacin da haka ya gaza ta koma bangaren lalata dukiya.
Rana ta musamman a wajen tseren dawaki
Ranar 4 ga watan Febrairun 1913 ta zama wadda ta sauya tarihin gwagwarmayar. Emily Davison ta sabule ta shiga cikin inda ake gasar tseren. Saboda ta janyo hankalin mutane kan fafutuka da mata suke yi.
Ya zama babban abu mai jan hankali
Haka ya samu nasara. Wajen tseren dawaki ba sarakuna kadai suka halarta ba, har da wakilan kafofin yada labarai masu yawa wadanda suka ruwaito lamarin gami da hotunan da aka dauka lokacin.
Zaman makoki kan juriya
Emily Davison ta mutu saboda raunikan da ta samu. Mutane da dama sun halarci jana'izzar a birnin London. Gwagwarmayar matan ta kara karfi.
Sannu a hankali nasara ta samu
Hakan ya kawo karshe a ranar 6 ga watan Febrairu 1918, inda 'yan gwagwarmayar suka samu nasara. A wannan lokaci an kafa doka kan 'yancin mata na kada kuri'a. Dokar amma ta takaita zaben ga mata masu dukiya da wadanda shekarunsu suka haura. Kafin samun cikekkiyar dama sai da aka gabatar da jawabai fiye da 10,000 da mataki na hakika.