1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan yaki da jahilci a Najeriya da Nijar

Ramatu Garba Baba MAB
September 8, 2017

Wasu 'yan asalin Bauchin Najeriya na daukar dawainiyar gina makarantu a wani matakin inganta ilimi, yayin da makarantu masu zaman kansu na Nijar ke kara kudin makaranta, a daidai lokacin da ake yaki da jahilci a duniya.

https://p.dw.com/p/2jcAg
Äthipien - Bücher für Afrika - Bücherspende
Hoto: privat/Abebe Kebede

kasashen Najeriya da Nijar sun bi sahun sauran kasashen duniya wajen tunawa da wannan rana mai matukar muhinmanci a rayuwar kowacce al'umma, Najeriya da Nijar musanman sun dadde a yunkurin kawar da jahilici a tsakanin al'umma idan aka yi la'akari da gudumuwar gwamnatoci wadannan kasashe dama na bangaren kungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafa wa jama'a musanman yara don ganin sun sami ingantancen illmi. 

A wani abu da ke nuna irin ci gaban da aka samu a fannin inganta illmi a jihar Bauchi da ke a arewacin Najeriya, akwai daidaikun makarantu da wasu 'yan asalin jihar suka dauki dawainiyar  ginawa  a wani mataki na yakar jahilci a wannan jahar, kuma wadannan mutanen  da suka yi wannan kokarin sun ci gaba da kokarin kulawa da duk gyara da ake bukata a makarantun domin kaucewa duk wata matsala da ka iya kawo tarnaki ga harkar ilimi.
A Jamhuriyar Nijar ma kasar ta bi sahun sauran kasashen duniya wajen bikin tuni da wannan rana don wayar da kannun al'ummar kasar kan mahinmanci ilimi ga rayuwar dan adam. A daya bangaren kuwa batun makarantu masu zaman kansu a  kasar na kara kudadden karatu a duk shekara duk yadda suka ga dama duk da kokowar iyayen yara ya kasance wani lamari da ake ganin ya kamata gwamnati ta shigo ciki don takawa wadannan makaratun masu zaman kansu  birki. Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen Afrika inda ake da kaso ashirin da uku cikin dari kacal da suka iya rubutu ko karatu, yanzu haka ma gwamnati ta fito da shirin karantar da mutanen karkara har ma da na birane wadanda ba su samu nasarar zuwa makarantar boko ba inda ake amfani da harsunan kasar kamar su Hausa da Fulatanci da Zabarmanci da kuma Buzanci bisa yankunan da mutanen ke rayuwa a ciki.

Stephanie Sinclair - Gewinnerin des Anja Niedringhauspreis 2017
Hoto: IWMF/Stephanie Sinclair