Matakan yaƙi da ɗumamar yanayi | Siyasa | DW | 04.05.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matakan yaƙi da ɗumamar yanayi

Ƙurrarun masana sun bayyana rahoton matakan yaƙi da gurɓacewar yanayi

default

ƙurrarun massana ta fannin yanayi sun tabbatar da cewa, ƙasashen dunia na da hanyoyin magance matsalar ɗumamar yanayi da gurgusuwar hamada.

Massanan sun gabatar da wannan bayyani, a cikin rahoton da su ka hiddo, a ci gaba da taron da su ke gudanarwa, a birnin Bangkok na ƙasar Thailand.

Kurrarun da su ka zo daga ƙasashe daban-daban na dunia na masanyar ra´ayoyi a game da hanyoyin bi, domin kare dunia daga ɗumamar yanayi, da kuma gurgusuwar hamada da ke matsayin babbar barazana, ga rayuwar bani Adama, tsirai da dabbobi a doran dunia.

Rahoton da su ka bayyana ya nunar da cewa, babu shakka dunia na da damar samun kariya ga wannan bila´i tare da yan kudaden da bas u taka kara sunkarya ba,to amma da sharadin a fara ɗaukar matakan da su ka dace ba da bata lokaci domin a cewar su ƙarfe da zafi ake bugun sa domin bashi suppar da ake buƙata.

Shugaban hukumar kasa da kasa mai kulla da yaki sda dumamar yanayi Ogunlade Davidsonya ce mudun ƙasashendunai su ka ci gaba da yin burus da matsaloin tabarbarewa yanayi,ko shakka babu, dunia zata shiga wani matsayi inda rayuwa z ata matukar wahala.

Nan da shekaru 20 zuwa 30 masu zuwa dunia na cikin barazana inni wannanrahoto, yanzu dubara ta rage ga mai shiga rijiya injhiu rahoton au magabatan dunia sun ware kudaden yaki da matsalar, au kuma su yi burus da ita.

Sarrafa hasken rana da iska domin samar da wutar lantarki na da sahun gaba na matakanyaki da dumamar yanayi inji rahoton.

A cewar Frank Asbek wani kurraen ta faninilimin dumamar yanayi a annkasar Jamus babu makawa cilas sai an yi anfani da zafin rana wajejnsamun makamashi muddun a na bukatar cima tudundafawa.

………………………………………………………………….

Nan da shekara ta 2020 mu na iya tsinmin fiye da kashi 35 bisa 100 na makamashi idan mu ka yi anfani da hasken rana.

„Nan da shekaru kima nin100 da su ka wuce a ka gano man petur da Kol wajen samar da makashi, to amma a kawana a tshi wannan ma´adanai ƙarewa za suyi , cilas tun yanzu mu fara sabawa da yin dogaro da hasken rana, wannan itace hanayar yaki da dumamar yanayi babu makawa“.

Anfani da zafin rana zai taimaka wajen raguwar yaɗuwar gurɗatacen iskan gaz, a sararin dunia, wanda shine ummal ib´isar hadasa ɗumamar yanayi.

Wani matakin kuwa, ya jiɓanci rage saran itatuwa na barkatai.

Mahalarta taron na Bangkok, sun nuna rashin gamsuwa a game da yadda wasu ƙasashe da su ka haɗa da Sin da Amurika ke yin ƙafar angullu ga wannan batu mai mahimmancin ga rayuwar ɗan adama doran dunia.

A halin yanzu hankullla sun karkata ga taron ƙungiyar G8 da zai gudana a nan kasar Jamus a wata mai kamawa.

Albarakacin wannan taro a na kyauttata zaton ƙasashen masu faɗa a ji, za su bayyana sanarwar haɗin gwiwa a game da batun ɗumamar yanayi.

 • Kwanan wata 04.05.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btvc
 • Kwanan wata 04.05.2007
 • Mawallafi Yahouza S. Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btvc