Matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Girka ya fara janyo martani | Siyasa | DW | 03.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matakan tsuke bakin aljihun gwamnatin Girka ya fara janyo martani

Ko wane lokaci daga yanzu dai ana saran ƙasar Girka zata samu kuɗaden ceto

default

Jean Claude Juncker

Kafofin yaɗa labarun Girka sunyi gargaɗi dangane da mawuyacin hali da ƙasar zata faɗa, yini guda bayan gwamnati ta sanar da matakanta na tsuke bakin aljihu, a madadin ƙudaden ceto da zata samu daga ƙungiyar Tarayyar Turai da hukumar bada lamuni ta IMF.

Jaridun Girkan dai, sun rubuta sharhuna daban-daban game da batun matsananciyar rayuwar da al'ummar ƙasar zata shiga sakamakon shirin kowa ya ji a jika da hukumomin suke aiwatarwa, inda jaridar Ta Nea, wadda ke goyon bayan manufofin gwamnati ta ambata cewar: " Yanayin rayuwar mu, na ma'aikata, da mabuƙata, da kuma masu tsara rayuwarmu baki ɗaya a wannan ɓangare na yankin Balkan, a yanzu tamu ta ƙare tun a jiya."

Wani kan labarin da jaridar Independent ta rubuta kuwa cewa yake: " Zamu yi tsawon shekaru huɗu ba tare da numfasawa ba."

Matakan tsuke bakin aljihun da jaridun ke magana akai dai sune rage Euro miliyan dubu 30 cikin kasafin kuɗin ƙasar nan da shekaru ukku masu zuwa, wanda ya tanadi ragin albashin ma'aikata, da kuɗaɗen sallamar ma'aikatan da suka yi ritaya, game da ƙara kuɗin haraji, kana da tsawaita shekarun bayar da gudummuwa ga asusun Fanshon ma'aikatan, inda kafofin yaɗa labaran ƙasar ke cewar, a duk lokacin da aka sami wata matsala, to kuwa ma'aikatan ne ke fuskantar raɗaɗin, ko da shike kuma jaridun sun ƙara da cewar, tilas ne gwamnatin ta ɗauki matakan domin kaucewa taɓarɓarewar tattalin arziƙin baki ɗayan sa.

Memoclick Brasilien Jose Manuel Barroso, Präsident der Europäischen Kommission

Jose Manuel Barroso

Gungun ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗi ta Euro ne suka gudanar da taro a birnin Brussel na ƙasar Beljiam, inda suka amince da ware kuɗi Euro miliyan dubu 110 cikin shekaru uku - a matsayin rance ga ƙasar ta Girka.

Shugaban gungun ƙasashen, kana Frime ministan Luxembourg Jeaun - Claude Juncker shi ne ya shaidawa manema labrai hakan bayan kamala taron:

"Ƙasashe 16 dake amfanin da Euro sun amince da cimma yarjejeniya dangane da ƙuɗaden ceton. Hakan ya biyo bayan rahotan da babban Bankin turai da hukumarta suka gabatar ne dangane da irin barazanar faɗuwar daraja da kudin Euro ke fuskanta"

Girka dai, ta sami rancen ne bisa tsauraran ƙa'idojin da shugaban hukumar Tarayyar Turai Hose Manuel Barroso ya ce sum gamsu da gindaya su:

" Hukumar Tarayyar Turai na ganin cewar, a yanzu an cimma sharuɗɗan da Turai ta gindaya domin baiwa Girka rance. Muna so kuma mu bayyana a fili cewar, za'a biya dukkan buƙatun ƙasar Girka."

Matakan da tarayyar Turai ɗin ta ɗauka dai, na da nufin hana yaɗuwar rikicin tattalin arziƙin Girkan ne ya zuwa sauran ƙasashen dake cikin ƙungiyar, inda Jamus ce zata bayar da kaso - mafi tsoka daga cikin adadin kuɗi Euro miliyan dubu 80n ɗin da gungun ƙasashen dake amfani da Euro zasu bayar. Lamarin da ministan kula da harkokin kuɗi a Jamus Wolfgang Schäuble ya ce na da muhimmanci

Jean-Claude Trichet Wolfgang Schaeuble Dominique Strauss-Kahn

"Dukkan Turawa da Jamusawa da suma turawan ne ,na da manufa guda na cimmawa, wanda shine abunda muka yi a nan na tabbatar kare darajar Euro, a yankunan da ake amfani da shi gaba daya. Wannan nauyi ne daya rataya a wuyammu. Ingancin aikimmu nada muhimmanci ga turai dama Jamusawa baki ɗaya"

Tarayyar Turai ta cimma wannan matsayar ce, bayan jerin tarukan da shugabannin ƙungiyar suka yi tare da asusun bayar da lamuni a Duniya na IMF, wanda zai baiwa Girkan rancen Euro miliyan dubu 30 kenan - nan da shekaru ukkun.

Mawallafi: Umar Saleh Saleh

Edita: Zainab Mohammed