1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan tsaro a Yuganda domin taron AU

July 24, 2010

Yuganda ta tsaurara matakan tsaron da ba'a taɓa ganin irin sa ba domin taron shugabannin ƙasashen AU

https://p.dw.com/p/OTtb
Hoto: AP

Hukommi a ƙasar Yuganda sun tsaurara matakan tsaro a jajiberin taron ƙungiyar tarayyar Afirka AU da zai gudana a gobe Lahadi - idan Allah ya kaimu. Shugabanni daga ƙasashen Afirka daban daban ne suka fara isa Kampala babban birnin Yuganda domin halartar babban taron, wanda zai sami halartar fiye da shugabanni 30, kana ke zuwa makonni biyu bayan ƙaddamar da tagwayen hare-haren bama baman da ƙungiyar Al-Shabab ta ƙasar Somaliya ta yi iƙirarin kaiwa a birnin na Kampala, wanda kuma a cikin sa mutane 76 suka rasa rayukansu.

Muƙaddashin ministan kula da harkokin wajen Yuganda Okello Oryem, ya shaidawa manema labarai cewar, sakamakon harin bam na ranar 11 ga watan Yulinnan, hukumomin na Yuganda sun tsaurara matakan tsaron da ba'a taɓa ganin irin sa ba, ko da shike a cewar sa abin baƙin ciki ne cewar hakan yana yin karan tsaye ga 'yancin mutanen da basu ji ba, ba su gani ba.

Tuni dai da ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar suka gudanar da tarukan share fagen babban taron, wanda shine karo 15.

A wannan wannan jiƙon dai taron zai mayar da hankali ne kan yawan mace macen mata da ƙananan yara da ake samu a lokacin haihuwa a nahiyar ta Afirka.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Mohammad Nasiru Awal