1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan tsaro a Jamus

November 19, 2010

Hukumomin tsaro a Tarayyar Jamus sun ƙarfafa matakan tsaro a filayen saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ƙasa

https://p.dw.com/p/QDGw
Ƙarfafa matakan tsaro a JamusHoto: dapd

A Jamus, ministan kula da harkokin cikin gida Thomas de Maiziere wanda ya sanar da barazanar da ƙasar ta ke fuskanta na ta'addanci a ranar Laraba bayan da na'urorin bincike su ka gano wata jaka da ke ɗauke da sinadiran bama-bamai a filin saukar jiragen saman Windhoek da ke Namibiya, ya ce mutane su zauna cikin hattara saboda har yanzu dai, suna fuskantar barazanar hari makamancin wanda ya auku a shekarar 2008 a birnin Mumbai da ke Indiya inda mutane 166 suka rasa rayukan su.

De Maiziere wanda ya yi wannan jawabi a wani gidan talabijin na nan Jamus ya ce mutane su cigaba da aikin su yadda su ka saba amma suna la'akari da yiwuwar wannan harin.

A yanzu haka dai an baza jami'an tsaro a filayen jiragen sama da na ƙasa a duk faɗin ƙasar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi

I