1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nato: Turkiyya na jan kafa kan Sweden

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2023

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa yana tsammani Sweden za ta dauki tsattsauran mataki kan yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4Tn73
NATO | Taro | Vilnius | Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip ErdoganHoto: LUDOVIC MARIN/AFP

Batun dakar tsattsauran mataki kan yaki da ta'addancin dai, na cikin yarrajejeniyar da suka cimma a tsakaninsu da za ta sanya Ankara amince Stockholm ta shiga cikin kasashe mambobin kungiyar Tsaro ta NATO. Da yake jawabi yayin taron kungiyar ta NATO a birnin Vilnius fadar gwamnatin Lithuania, Erdogan ya ce Sweden za ta mara wa Turkiyyan baya a kokarin da take na ganin an cimma yarjejeniya kan batun gyara a fannin hana fasa-kwabri da kuma samun damar yin tafiye-tafiye a kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU ba tare da takardar izini ba wato Visa. A hannu guda kuma, Erdogan din ya ce kasarsa za ta yi kokarin shiga tsakani domin tabbatar da ganin an cimma yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin da Rasha da Ukraine ke gwabzawa a tsakaninsu.