Matakan rigakafin murar aladu a Jamus | Siyasa | DW | 28.04.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matakan rigakafin murar aladu a Jamus

Kawo yanzu ba a tabbatar da ɓullar cutar murar aladu a nan Jamus ba. To amma gwamnatin Jamus ta jaddada cewa ƙasar ta kammala dukkan tanade-tanaden da suka wajaba don tinkarar cutar idan har ta kunno kai a ƙasar.

default

Binciken kan murar aladu a Jamus

A nan Jamus dai an samu mutane uku da ake kyautata zato sun kamu da ƙwayoyin cutar murar aladu. A halin yanzu ana bincike kan jinin mutanen waɗanda ba su daɗe da dawowa daga ƙasar Mexiko ba kuma an sa ran samun sakamakon binciken a gobe Laraba. Idan har aka gano ƙwayoyin cutar a cikin jininsu bai kamata a ta da hankali ba inji ƙaramin sakatare a ma´akatar kiwon lafiya ta tarayyar Jamus Klaus Theo Schröder.

Ya ce: "Ko da an samu masu ɗauke da ƙwayoyin cutar wanda abu ne mai yiwuwa daga cikin Jamusawa ´yan yawon buɗe ido 9000 dake Mexiko hakan ba ya nufin annobar cutar ta ɓulla a wannan ƙasa, domin hakan zai shafi ɗaiɗaikun mutane ne wanda kuma za mu iya ɗaukar nagartattun matakai cikin gaggawa don daƙile yaɗuwar sa."

Mexiko Schweinegrippe Passanten mit Mundschutz

Ko da yake ƙwayar cutar sabuwa ce amma ana iya yin maganinta da magungunan mura ta yadda za a iya maganinta a Jamus ba da wata matsala ba. Bugu da ƙari ƙwarrarun likitoci sun tabbatar cewa ƙarfin murar na raguwa matuƙa a wajen ƙasar Mexiko. Yanzu haka wata tawagar ƙungiyar Lafiya Ta Duniya WHO na gudanar da bincike don gano musababbin a ƙasar ta Mexiko. A dangane da haka jami´in na ma´aikatar kiwon lafiya ta Jamus Klaus Theo Schröder ya ce cutar ta jurar aladu ba za ta zama wata annoba a duniya baki ɗaya ba.

Ya ce: "Har yanzu Ƙungiyar WHO ba ta yi magana game da annoba kuma har yanzu ba ta yi gargaɗi game da tafiya zuwa Mexiko ba to sai dai kamar yadda muka yi ita ma ta ba da shawara da a dakatar da tafiya zuwa Mexiko."

BdT Schweinegrippe

A dai halin da ake ciki ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta gargaɗi ´yan ƙasar da su guji zuwa Mexiko. A yekuwar da take yi dai gwamnatin tarayya na mayar da hankali musamman akan likitoci da masu kyamis da kuma matafiya. Duk wanda zai je Mexiko ko kuma ya dawo daga Mexiko a filayen jiragen sama ana ba shi takarda mai ƙunshe da muhimman bayanai game da cutar.

Ko da yake kawo yanzu ba wata allurar rigakafin wannan sabuwar ƙwayar cutar amma Farfesa Jörg Hacker na cibiyar nazarin kimiyya ta Robert Koch ya ce nan ba da jimawa ana iya samun wannan allura.

Ya ce. "Ko da yake ya zuwa yanzu ba mu gamsassun bayanai ko allurar rigakafin da muke da ita za ta yi tasiri, amma muna tattaunawa da ƙungiyar WHO game da samar da wata allurar rigakafin wannan cuta. Akwai ɗakunan binciken kimiyya a duniya baki ɗaya waɗanda za su iya yin bincike bisa manufar samar da rigakafin ta murar alladu."

Jamus kuwa na iya taka rawa a wannan fanni domin ƙasar na wurin samar da irin wannan allurar rigakafi mafi girma a Turai baki ɗaya. A halin da ake ciki masana a ƙasar sun haƙiƙance cewa murar alladun na yaɗuwa tsakanin ɗan Adam zuwa ga ɗan Adam amma ba tsakanin alade zuwa ga ɗan Adam ba. Saboda haka ga masu cin naman alade babu wata damuwa game da amfani da naman.

Mawallafa: Nina Werkhäuser/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmad Tijani Lawal