1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan murƙushe ta'addanci

July 7, 2010

A ƙasashe da dama dake da ci gaban masana'antu ana fama da matsalar 'yan ta'adda renon gida

https://p.dw.com/p/ODN6
Harin ta'addanci a jiragen ƙarƙashin ƙasa a LondonHoto: AP

Batun 'yan ta'adda na cikin gida, abu ne da a shekaru biyar da suka gabata aka fara jinsa lokacin da aka kai hari kan jiragen ƙasa a birnin London, wanda ya halaka mutane 56, wasu kimanin 700 suka jirkata. A shekarun ne kuma wani harin ta'addanci a ƙasar Spain ya halaka mutane191, wanda shi ma mutane 1460 suka samu rauni, haka a ƙasar Jamus an samu waɗanda suka shirya kai harin ta'addanci, inda duka waɗannan aka kwatanta su da 'yan ta'adda ne daga cikin ƙasashen.

Su dai waɗanda suka kai hare hare a nan Turai sun sha bamban da na harin sha ɗaya ga watan satumban shekara ta 2001. Akasarinsu dai sun girma ne a waɗannan ƙasashen, a nan suka yi makarantu, wasun su sun zo ƙasashen ne da iyalansu, waɗanda ba masu tsattsauran ra'yin addini ba ne, kai wasunsu ma ba su da asalin musulunci, wato dai sun musulunta ne kuma daga baya ne suke haɗuwa da masu tsananin kishin addini waɗanda suke juya musu ƙwaƙwalwa.

Magnus Ranstorp wani malami ne a cibiyar tsaro dake Stockholm a ƙasar Sweden ya kuma bayyana darasin da aka koya.

Helkwatar 'yan sandan Birtaniya na ta yin ƙoƙari sosai wajen yaɗa labarin a nan take, ba tare da jinkiri ba. 'Yan sandan sun yi ƙoƙarin kwantar da hankalin mutane, nan take bayan harin amma dai akwai matakai masu ƙarfi da hukumomi ya kamata su ɗauka. Dole ne al'umma ta riƙa kula da mutane masu tsttsauran ra'ayi dake unguwanninsu.

Samun haɗin kai tsakanin jami'an tsaro da al'ummomi wani muhimmin abu ne wajen tabbatar da tsaro mai inganci. Kamar yadda Ole Schröder dake ma'aikatar cikin gidan Jamus ya bayyana.

"Yana da muhimmanci mu yi aiki tare da mazauna unguwannin da masu tsattsauran ra'ayi suke, kamar ƙungiyoyin masallatai da dai sauran wuraren da masu tsattsauran ra'ayin ke taruwa"

Abu mafi muhimmanci, shi ne a riƙa koya wa limamai dake jagurantar masallatai darussa, kan yaƙi da tsattsauran ra'ayi, inda zasu sauya ra'ayoyinsu daga yakoma masu natsuwa. Kana yakamata a samar da sasantawa sakanin ƙasashen yamma.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmad Tijani Lawal