Matakan Majalisar Dinkin Duniya sun gaza a lardin Darfur | Labarai | DW | 14.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakan Majalisar Dinkin Duniya sun gaza a lardin Darfur

Duk kokarin da aka yi kawo yanzu da nufin samar da zaman lafiya a lardin Darfur mai fama da rikici a yammacin kasar Sudan ya citura, inji wakilin MDD Jan Pronk. A lokacin da yake magana a gaban kwamitin sulhu, Mista Pronk ya ce dole ne MDD ta amsa cewar dukkan dubaru da matakan da take dauka akan lardin Darfur sun kasa haifar da da mai ido. Pronk ya ce ana bukatar sojojin kiyaye zaman lafiya kusan dubu 20, domin a kwance damarun sojin sa kai tare da tabbatar da komawar fiye da ´yan gudun hijira miliyan biyu yankunan su na asali. Yanzu haka dai kungiyar tarayyar Afirka AU ta girke dakarun wanzar da zaman lafiya kimanin dubu 7 a lardin na Darfur. Kungiyar ta AU dai na goyon bayan shirin girke dakarun MDD a wannan yanki. To amma gwamnatin Sudan na adawa da shirin, tana mai cewa sojojin kungiyar AU din sun wadatar.