Matakan kyautata matsayin mata a kasar Liberia | Zamantakewa | DW | 25.11.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matakan kyautata matsayin mata a kasar Liberia

A Liberia, shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta fara daukar matakan kyautata matsayin mata

default

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta kasar Liberia

Jagora ko kuma mace ai kamar maza ta Afrika. Wadannan suna daga cikin sunayen da akan kira shugaban kasar ta Liberia, Ellen Johnson Sirleaf dasu. Shugaban kasa ta farko mace a nahiyar Afrika, ko kadan bata kyale wasu su nuna shakkar cewar a matsayin ta na mace, ita ce tafi dacewa ta shugabanci kasar fiye da ko wane namiji ba. A hirarraki da ita, tasha nuna cedwarf a nahiyar Afrika, mata, ba kamar takwarorin su maza ba, tun suna kanana sukan koyi daukar nauyi kula da rayuwar wadanda suke kusa dasu, su dauki nauyin aikin gida da kula da iyali.. Saboda haka tace bukatun kare mata, suna daga cikin manyan al'amuran da suke da muhimanci a gareta. Kare mata daga duk wnai cin zarafi, shine tushen rayuwar duk wata al'umma inji Ellen Johnson, dake shugabancin kasa mai fama da talauci da tayi shekaru 25 karkashin mulkin soja da kuma shekaru golma sha hudu da yakin basasa.

Fyade ga mata babban abu ne a garemu. Mun fito ne daga wani yanayi na yakin basasa tsawon shekaru masu yawa, inda tsakanin wadannan shekaru duk wnai mutunci dfa darajar dan Adam aka yi w. Mata an rika yi masu fyade, an maida su bayi, yan mata an rika sace su ana cin zarafin su. Saboda haka ne yanzu, fyade a garemu ya daina zama dan karamin laifi, duk kuwa wanda aka samu dashi, ana iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

To sai dai kuma har yanzu maza sune wuka sune nama a tsarin shari'ar Liberia. Saboda haka ne za'a dauki lokaci mai tsawo kafin wadannan tsauraran dokoki na huikunta masu laifin fyade su fara zama masu amfani da mata da akai wa wannan laifi. Duk da haka, Ellen Johnson Sirleaf tace mata tilas a kare su daga fyade, wadda zasu sami damar tafiyar da rayuwar da aiyukan su cikin kwanciyar hankali.

Tace wajibine a fara wnanan aiki daga tushe, saboda haka ne muka fara da yan mata. amma bamu tsaya a nan ba, domin kuwa har yara maza matasa suma ba'a bar su a mbaya ba. Mun maida hankali domin ganin a matakan da muke dauka, mun daidaita tsakanin maza da mata tun daga makarantun piramare. Saboda haka ne muka maida shiga makaranta ya zama tilas a makarantun gwamnati. Mun kawar da biyan kudin makaranta, abin da ya sanya muka sami karin yara dake shiga makarantu.

Ilimi, kamar yadda shugaban ta Liberia take gani, bayan kare mata daga cin zarafin su, shine abuna biyu da zai taimakawa samun daidaituwa tsakanin maza da mata a nahiyar Afrika. Tace sannu a hankali tana ganin canjin da ake samu ta wnanan fuska.

Tace ina da ra'ayin cewar a duniya baki daya ana samun canjin yanayi, inda mata suke kasancewa a halin da zasu dauki matsayin da ya dace dasu a rayuwar yau da kullum. Matan sukan nemi hakkin su su tsaya sai sun smi hakkin nasu.

To sai dai tace har yanzu yan siyasa maza da mata a ko ina cikin duniya suna da sauran gagarumin aikin dake gaban su. Alkawuran da suka yi a da can ma ba'a cika su ba, kamar misali, a lokacin taron mata na duniya da majalisar dinkin duniya ta shirya a Peking a shekara ta 1995.

Tace da yawa daga cikin mu, mun gabatar da wani shiri na kyautata matsayin mata a lokacin tzaron na Beijing. To amma ina iya cewar aiwatar da wannan shiri, ko kadan bai kusanci yadda muke sa rai zai yi a daidai wnanan lokaci ba.

Ellen Johnson Sirleaf tace kungiyoyin mata suna da mmuhimiyar rawar da zasu taka a game da kyautata matsayin mata a rayuwar yau da kullum. AKwai matakai da dama da ake iya dauka, domin karfafa aiyukan irin wadannan kungiyoyi, musmam,an yadda zasu kyautata aiyukan su, musmaman a wuraren da cin zarafin mata ya zama ruwan dare.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Tijani Lawal