Mataimakin Firaministan Iraqi yace janyewar sojin Amurka daga kasar zai jefa kasar cikin sabon bala′i | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mataimakin Firaministan Iraqi yace janyewar sojin Amurka daga kasar zai jefa kasar cikin sabon bala'i

Mataimakin Firaministan kasar Iraqi Barham Salih yayi gargadin cewav gagauta janye sojin Amurka daga kasar zai zama balai ga Iraqi yana mai kira kuma ga Kungiyar Taraiyar Turai data taimaka sake gina kasar.

Barham ya fadawa komitin kula da harkokin waje na kungiyar a Brussels cewa har yanzu basu da karfin fuskantar kalubale na tsaron kasar dake gabansu,saboda haka janyewar sojin Amurka zai jefa kasar cikin wata sabuwar matsala.

Yanzu haka dai akwai sojin Amurka 144,00o dana Burtaniya 7,200 dake Iraqin.

Tun lokacinda Amurkan tab mamaye Iraqi ana ci gaba da samun tashe tashen hankula na bangarori dabam dabam a kasar,amma Barham salih yace yana fatar kasashen duniya ba zasu yi anfani da batun tashe tashen hankula a airaqi ba a matsayin hujja na ficewa daga Iraqin.

Ya kuma roki kashen Kungiyar Taraiyar Turai da su kara bada taimakonsu ga kasar.